WAFATIN ANNABI SAW (5)
MANZON
YA FARA RASHIN LAFIYA:
Ya gabata
garemu cewa sadda Manzon (SAW) ya dawo daga Hajji, sai yaji ciwon kai iri na
matafiya bayan 'yan kwanaki ya warke, sai kuma cikin watan safar wajejen 29 –
ko 28 ya fara rashin lafiyar da yayo wafati a cikinta.
A
farkon rashin lafiyar sa Manzon (SAW) ya fara da ciwon kai, kuma ya zamo yana
ciratuwa daga dakin waccan matar tasa, zuwa waccan, daga karshe rashin lafiyar
sa tayi tsanani a dakin Maimunatu bintil Haris, sai ya tara matansa ya nemi
izininsu kan yayi jiyyarsa a dakin S. Aisha (RTA). Sai suka yarda da Shugaban
Adalai SAW.
MUTANEN
MADINA AL-ANSAR DA TSORON RABUWARSU DA MANZON (SAW):
An
rawaito sa'adda Manzon Allah (SAW) yake rashin lafiya har ya kasa fitowa
sallah, sai mutan Madina wato Ansaru suka taru a cikin masallacin Manzon (SAW),
suna masu tausayawa da kuma tsananin tsoron ace Annabi (SAW) ya bar duniya.
Saboda haka Abbasu dan Abdulmuttalib (RA) ya shigo ya sanar da Manzon Allah (SAW)
abinda suke ciki, nan take Annabi (SAW) ya fito kansa a sunkuye ya dafa S. Ali
da Fadlu, Abbasu kuma a gabansa, har sai da ya isa bakin Minbarinsa ya zauna,
sannan mutane suka zauna suka nutsu sai ya godewa Allah ya yabeshi, sannan yace
"yaku mutane labari ya isar min cewa ku kuna tsoron mutuwar Annabinku,
shin an wanzar da wani Annabi gabanin zuwana? Balle ni a wanzar dani a cikin
ku? To kusani nifa mai haduwa ne da Ubangijina, haka kuma masu haduwane dani,
saboda haka ina yi muku nasiha da muhajirai na farko da alheri…. Ina yi mumu nasiha
da Ansaru da alheri domin sune wadanda suka tanadi gida da imani gareku, ku kyautata
musu, ba sune suka raba yayan itacensu daku ba? Ba sune suka yalwata muku a
cikin gidansu ba ba sune suka zabeku akansu ba?! suka baku abubuwansu koda suna
da bukata?! Sai Sahabbai suka rushed a kuka, daganan mazon Allah (saw) ya koma
gida.
Comments
Post a Comment