Fassarar jawabin wani Limamin Harami kan Maulidi.


Shi wannan Limami sunansa DR ADEL AL KALBANY daga baya an cireshi daga Limanci saboda sabanin fatawarsa data sauran Malaman kasar Saudi Arabia, kuma yayi wannan Jawabi ne a cikin shekarar 2013. Duk da cewa ba dukkan jawabin ne ya dace da raayina ba, amma wannan jawabi akwai adalci a cikinsa musamman ga masu yin Maulidin Annabi saw ga jawabin:

MAULIDIN ANNABI SAW

DR ADEL AL KALBANY
Fassarar Tahir Lawan Muaz Attijaneey

Arana irin ta yau kimanin Karni goma sha hudu da suka wuce Duniya ta samu wata daukaka da haihuwar Masoyi saw wanda wannan wani alkwarine  gareta dazai faru na haihuwarsa. Wannan alkawari shine tabbatuwar Aikensa da risala matabbaciya, da aike mai girma zuwaga dukkanin Mutane, kai bari izuwa dukkan Nauyaya biyu (saqalain) mutum da Aljan, tana yiwa muminai bishara, tana yiwa Kafirai gargadi, tana mai tunatar dasu ranar Alkawari.
“An haifi shriya don haka kasantattu sun zamo haske## Bakunan samammu sai murmushi suke da Haske,” (wannan baitine na kasidar shugaban mawaka Ahmad Shauqy)
A watan R/Auwwal Kissar Karshen Zalunci da tada karan Hanci ta fara, adai cikin wannan wata na rabiul Auwal ne Risalar nan ta Musulunci mai cikawa ta fara tana mai haskaka zamani , don farkon abinda Wahayin Annabi saw ya fara dashi shine RUUYA mafarki na gaskiya, ya zamo bai ganin wani abu face yazo masa tamkar kecewar alfijir, har zuwa lokacin da Jibrilu yazo masa da wadanna kalmomi dawwamammu (kai karatu da sunan ubangijinka wannan da yayi halitta) tsawon  wahayi yada Mafarkincan shine wata shida.
A cikin dai watan Rabiul Auwal dai Birnin Madina ta samu daukaka ta yadda kafarsa mai tsarki ta taka Turbayarta, haka dai babbar lokacin Musifa babba kuma ta sauko ta lokacin da hasken Ranar rayuwarsa ta fara alamun faduwa.Jayayya tana yawaita bisa alada duk shekara kan halaccin Maulidinsa saw yadda masu Khudba a masallatai suke tsautar da Mutane game da yin taron na Maulidi, amma wasu kuma suna ci gaba da wannan taro a sassan kasashen Musulmi cikin Duniya.
Abinda nakeson nai ishara dashi kuma na karfafa shi anan shine, in muka kauda kai daga wannan jidali baki dayansa kan Taron Maulidi, abune da babu jayayya akansa shine Annabi saw ya kasance haske ne, kuma wata tocilan ce da ta haske hanyarmu mukaga komai,  muka gane hanya,  kuma babu kokonto cewa soyayyarsa tana nan a dankare a karkashin zuciyoyin muminai, haka shaukin ganinsa buri ne da bazai gushe ba a zuciyoyin Musulmi har ma Fasikansu, balle ma ace Masu Tsoron Allah. Babu kuma hanya ta samuwar hakan saida bin Sunnarsa da kuma riko da hanyarsa da barin kirkirar bid’oi a shariarsa.
Amma kuma ai itama munasaba (wani lokaci day a dace da wani day a gabata) tana da nata bigiren a cikin tunatarwa, kuma tana da matukar tasiri, shiyasa sadda aka tambayi Annabi saw game da azumin ranar Litinin sai yace “Wannan ranace da aka haifeni cikinta wannan wuni ne da aka aikoni cikinsa,” muslim ne ya rawaito shi. Lokacin da Birnin Madina ya daukaka da zuwan Annabi saw kuma ya tabbata cikinta ya samu yahudawa suna azumin Ashura, sai ya tambayi dalili, sai akce dashi wannan Wuni daaka nutsar da Fir’auna cikinsa aka kuma tsrear da Annabi Musa AS. Don haka muke azumtarsa don godiya ga Allah, sai Annabi saw yace ai kuwa mune mafi cancanta da Musa fiye daku sai ya Azumceshi kuma yai Umarni da a azumceshi.
Babban Malamin Hadisi Ibn Hajar yana cewa: “zamu fahimta daga wannan hadisi halaccin aikata godiya ga Allah kan wani abu da yai maka niima dashi a wani wuni sananne, na bada niima ko tunkude azaba.”
To in mukai gini kan wannan ni ina cewa bai klamata ga Musulmai su bari Shaidan ya ya jasu zuwa kirkirar bid’ah, amma kuma su tsautu kada tsoron fadawa bid’ah din ya zamo dalili ne na mancewa da kasha Sunnar Annabi saw da kuma tarihi da halayensa da shiryarwarsa.
Domin da yawa zamuji masu hana mutane yin bid’ar Maulidin Annabi saw suna cewa ai shi Annabi saw abin Ambato ne koda yaushe do haka (baza aware wani wata dan a amabaceshi ba kawai) kuma shi sirarsa ana karanta koda yaushe da abinda yaiu kama da wannan zantuka wanda suke kafa hujja dasu wanda kuma a zahiri ba zancene day a hau kan layi daidai ba, kai bari ma dai muce ba zancene ingatacce ba sam. Domin wasu zantuka mmasu yawa sun rijaya akansa , harma masu riya su mabiyansa ne sun zamo basa ambatonsa sai lokacin da zasu hana mutane yin Maulidi kawai, sannan shekara zata kare suna ta Magana akan wani maudu’in amma fa banda sirarsa da tarihinsa har ya zamo da zamu tambayi yayanmu game da Siffofin Annabi saw kai bama yayanmu ba mu tambayi kanmu wadannan siffofi nasa da abinda muka sani game da Sirarsa ko muka haddace na Sunnarsa  to lallai kam zaaga abinda mutane suka sani game da wawaye da banzayen mutane yafi abinda suka sani game da fiyayyen Manzonni saw don kuwa abinda muka sani bai taka kara ya karya ba.
To duk ka rabu da wancan musu da bashi da Amfani game da hukumcin yin Maulidin Annabi saw ka tambayi kanka sannan ka amsawa kanka tsakani da Allahyaushe ne ka karanta wani littafi na Sirar Annabi saw wane irin sani kake dashi game da dashi?  Kuma meye Nasabarsa saw? Kasan siffofinssa? Sannan kasan Matayensa da Yayensa? kasan me yake so da me yake ki? Kuma kasan wani abu mai fadi acikin rayuwarsa?
In ka amsa wannan tambayoyi zaka gano cewa fa shaidan na yaudararka da sunan SUNNAH sadda yai maka rudi da cewa karanta sirar Annabi saw zata jaka zuwa Sufanc ne kawai. Kuma soyayyar Annabi saw bat a Zuciya bace AA ta Biyayya ce. Sannan ka binkici kanka ka tarar wannan biyayya da yake rudarka da ita itace kawai Hana taron Maulidin Annabi sawsannan saba masa cikin Kamanninsa da Suunarsa, sai kaga ka fara samun Tawili har 20 wajen aske gemunka wanda da ka karant Sirarsa zakaga mai kaushin Gemanya ne, Kuma baya jan Tufafin a kasa, haka sahabbansa basu zamo suna tambayar wannan sunna ce da ake bawa mai aikata ta lada ba ko ai wa wanda ya barta azaba ba, aa kawai suna aikatawa ne don masoyunsu ya aikata suma suke aikatawa saboda soyayyarsa da kuma koyi dashi.
  Yayin da kai kuma kaje kake ta hakilon cewa baza ayi bid’ah ba bazamu ga wani abu ba a tare dakai ba wanda yake nuna mana cewa kai ma kana cikin mabiyansa, kaima sai shaidan ya samu abinda yake sota yuadda ya nisantaka daga Sunnarsa da sirarsa baki daya, ya kuma cika rayuwarka da waninsa. To don Allah ka gaya min ta ina ne zaka bi wanda bakan san komai ba a rayuwarsa? Sai dai dan abinda ka yafuto daga nan daga can. to ta yaya zakai fatan a tasheka tare da wanda zuciyarka bataji tana sonsa ba sai dai kawai daawah a baki? Da ka zamo mai gaskiya ne to da zaa ga alamunsa na bayyana tare da kai.
Hakika biyayyarsa saw ba aikine ba kawai daidai da yadda yazo dashi ba, bariu dole kuma sai ya zamo soyayya c eta zuciya, soyayya da zakaji tana yanka lokunan zuciyarka saboda Annabi saw yace “dayanku bazai imani ba sai nazmo nine mafi soyuwa gareshi fiye da yayansa da iyayensa da ma mutane baki daya” Muslim ne ya rawaito shi,Soyayyar Yyaye Da Iyaye kuwa ba soyayyace ba ta biyayya, bari dai Kauna ce ta rai wadda take can cikin Zuciya.
Bai kamata ace wannan wata na Rabiul Auwal yazo ya wuce ba baki dayansa ba tare da muntuna dashi ba, kuma mun karanta Sirarsa da karansa sunnoninsa ba, da yiwa kawunannmu nasiha game fuskantar tag a biyayyarsa ko tsaurin idonta cikin saba masa.
Don haka ka sanya wannan wata na Rabiul Auwal baki dayansa wata Munasaba ce ga wannan lamari har dai rayuwarkla ta daidaita akan Hanyarsa saw, zuciyarka ta cika da Kaunarsa, don wallahi bazaka samu tsira ba sai Zucirka ta kwaranya da sonsa da girmamashi. Ka kuma gode Allah bisaniimarsa ta kasancewarka cikin Alummarsa saw, kai kokari kuma a tasheka cikin Jamaarsa karkashin Tutarsa, kuma ka gangara tafkinsa, ka samu cetonsa,ka shiga Aljanna tare dashi, don mutum na tare da wanda yake so Kada wani daya ya rinjayeka cikin sonsa sannan kuma ka rika yiwa ranka burin ganinsa kai mata dabaibayi da sunnarsa.ka rera mata waka da sirarsa, kai mata fatan zama dashi, ka yawaita yi masa salati da sallama don ka samu rabauta da kasancewa tare dashi.
Ka sautrari siffofin wanda aka aiko don rahama ga talikai da fadin Allah inda yake bayani kan niimar da yayi garesu yana fadin:- “Hakik Manzo yazo muku daga cikinku, abinda zai wahal daku yana yi masa wahala, mai tsananin kwadayi ne cikin shiriyarku,mai jin kai ne da tausayi ga Muminai.
Ya Allah!!! Muna sonsa da yawa.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY