RAHAMAR TALIKAI ANNABI MUHAMMADU SAW
بسم الله الرحمن الرحيم وصلى الله على الفاتح الخاتم وعلى آله وصحبه حق قدره ومقداره العظيم وما أرسلناك إلا رحمة للعالمين Assalamu Alaikum Yan uwan Musulmi Masoyo Annabi SAW, ina taya mu murnar zagayowar wannan wata na haihuwar Shugaban kowa da koma Annabi Muhammadu SAW wanda ya zamo Rahama ce ga kowa da Komai. Hakika ba Musulmi kladai bane Annabi saw yazame musu Rahama ba, bari kamar yadda Allah ya fadawa Annabi saw cewa shi وما أرسلناك إلا رحمة للعالمين Bamu aikoka ba sai don ka zamo raha,ma ga dukkan Talikai, don halka yanzu ma iya dubawa mataki mataki mugano ta ina Annabi Muhammadu saw ya zamo Rahama ga Talikai? Don haka zamu iya kasa matakannan zuwa: 1. Annabi Rahama ne Ga Musulmi Wannan ba abu ne da yake a boye bag a kowane musulmi, don haka ba sai an fadada bayani akansa ma ba, ma iya takaitawa akan wadannan nuqdodi kamar haka: Kafin zuwan Annabi saw dukkan Halittu suna cikin bata saboda nisan su da Allah, Addinin Annabi brahim AS ya dusashe an can...