Maulidi a garin Makka shekara ta 823 karkashin Jagorancin Ibnil Jazary


Imamul Jazari Shugaban Makarantan Zamaninsa yana cewa:
"Haihuwar Annabi saw ta zamo a wuri da ake kira Shi'ib (wato Zaza) wuri ne sananne da yai tawaturi a garin Makka, mutanen Makka suna fitowa duk Ranar Maulidi sui biki mai girma fiye da bikin da suke da Sallar idi.
Na ziyarci wannan gida kuma na nemi albarkarsa shekarar da nai hajji wato hijra  792 kuma naga albarkar gidan da bazata kidayu ba.
Sannan na sake maimaita ziyararsa a shekara 823 lokacin danai zama Garin Makkah, a lokacin gidan da aka haifi Annabi ya rurrushe sai na sanya aka gyara shi, a ka kuma aka karanta littafina na Maulidi " ATTAARIF BIL MAULID SHAREEF" Jamaa da basu kirgu ba suka zo suka saurari littafin. Wannan Rana dai abar bada labari ce."

Daga Littafinsa ATTAARIF BIL MAULID SHAREEF" shafi na23.

Wani tsohon hoton gidan da aka haifi Annabi saw.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY