Maulud Nabiy: Gwamnatin Tarayya ta Sanar da Litinin Hutu na kasa

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa Litinin 12 ga Disambar nan a matsayin hutun Kasa don tunawa da Ranaar da aka Haifi Shugaban Kowa da komai Annabi Muhammadu saw
Hakan yazo ne ta bakin ministan harkokin cikin gida Gen Abdulrahman  Dambazau mai ritaya a yau dinnan Alhamis a birnin tarayya Abuja madadin gwamnatin.
A wata takarda mai dauke da sa hannun mai rikon sakataren ma'aikatar Alh Muhammadu Maccido Dambazau ya taya dakacin Musulmi murnar wannan Rana kuma yai kira dasu hada hannu da Shugaban kasa don gina gawurtacciyar Kasa mai cike da zaman lafiya.

A karshe ya bukaci yan kasar nan da sui amfani da wannan rana don yiwa Nigeria Adduoin zaman lafiya baki daya.

Sannan yai kira ga yan kasa da su cigaba da hakuri da kuma goyi bayan Gwamnati mai ci wajen tabbatar da aiwatar da ingataccen tsarin Kasa.

Eid-el-Maulud

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY