RAHAMAR TALIKAI ANNABI MUHAMMADU SAW
بسم الله الرحمن الرحيم وصلى الله على الفاتح الخاتم وعلى آله وصحبه
حق قدره ومقداره العظيم
وما أرسلناك إلا رحمة للعالمين
Assalamu Alaikum Yan uwan Musulmi Masoyo Annabi SAW, ina
taya mu murnar zagayowar wannan wata na haihuwar Shugaban kowa da koma Annabi
Muhammadu SAW wanda ya zamo Rahama ce ga kowa da Komai.
Hakika ba Musulmi kladai bane Annabi saw yazame musu
Rahama ba, bari kamar yadda Allah ya fadawa
Annabi saw cewa shi
وما أرسلناك إلا رحمة للعالمين
Bamu aikoka ba sai don ka zamo raha,ma ga dukkan Talikai,
don halka yanzu ma iya dubawa mataki mataki mugano ta ina Annabi Muhammadu saw
ya zamo Rahama ga Talikai? Don haka zamu iya kasa matakannan zuwa:
1. Annabi Rahama ne Ga Musulmi
Wannan ba abu ne da yake a boye bag a kowane musulmi, don
haka ba sai an fadada bayani akansa ma ba, ma iya takaitawa akan wadannan
nuqdodi kamar haka:
Kafin zuwan Annabi saw dukkan Halittu suna cikin bata saboda
nisan su da Allah, Addinin Annabi brahim AS ya dusashe an canza shi baki daya,
sannan Addinin kiristanci ya zamo addinin da Yahudu sukai kutu kutu suka canja
shi, don haka kowa ya shiga Dimuwa da ta sanya kowa neman inda Allah yake da
kansa, wasu sai suka duba sukace kai ai Ran ace don babu abinda ya kaita karfi
ita take bada haske da yake zama ENERGY ga kowa sai suka fara bauta mata. Wasu kuwa
sai suka ce Aaa ai babu wani Allah in banda Zamani shine yake zuwa da kowa ya
tsofar dashi ya kasha shi, sanmnan a sake haifar sa kuma, wadannan sune
DAHRIYYAWA Allah yana cewa a hakkinsu:
وقالوا ما هي إلا حياتنا الدنيا نموت ونحيثا وما يهلكنا إلا الدهر.
Wanda suka fi kowa wauta kumma sune wadanda suka zamo sun
sassaka wani abu da hannunsu suka ce shine
Allah, don haka gumaka suka cika Garuruwan Duniya Musamman Larabawan
Makka da Ta’if da makamantansu wadanda har kaaba suka sanyawa gumaka 360. Takai
mutum ya sassaka gunki na Dabino ya rika yi masa sujjada in yaji yunwa kuma ya
cinye ubangijin haka wanda yake da gunkin Azurfa ko Zinare in Talauci yaciushi
sai ya said a Allan nasa.
Ta fuskar rayuwa kowa ci barkatai yake, Mace ta auri Mutum
sama da Daya in ta haihu ta zabi wanda taga ya dace dashi ta dangana dan dashi,
Namiji kuma yana Gadon duk abinda Ubansa ya Bari hard a matayensa sais u zamo
matansa ko Bayinsa. Dalili karami na jawo Yakin shekaru 50 ai ta kasha juna
akan Rakumi ko tserten Doki wannan yaci wannan yai masa Rinto sai rigima a
shekara hamsin anay kasha juna.
Amma da zuwan Manzo saw sai wannan takau, ya kawo Allah
Musulmi da suke da rabo suka bishi ya kawo tsarin Rayuwa dababu wanmi addini da
yazo dashi, ya kwatowa Mata Hakkinsu, aka sanya musu gado aka dena Binne su
saboda tsoron talauci wanda a baya abin bah aka yake ba.
Ta fuskar sharia kuwa babu wata alumma data sami dace da
sauki da jin kai irin na Musulmi, ya ishemu Ishara cewa Alummatan baya sun zamo
suna Azumi ne na tsawon awanni 24 sai dai suci abinci sau daya kawai, da makamantan haka. Sannan du wani abui da
zai wahalar da Musulmi Manzo saw sai ya shiga yayiwa Allah kirari da dadin baki
an sauke mana shi, Kissar Sallolin 50 ta ishemu ishara, don haka Allh swt yake
masa kirari da fadinsa:
عزيز عليه ما عنتم حريص عليكم بالمةمنين رءوف رحيم...
Sannan Annabi saw yana cewa Ni An
aiko ni ne da Hanya mafi sauki, kana yana gayamana mubi Addininsa a sauki domin
sauki ne shi, wanda duk ya tsaurara to zaiga tsauri don Addinin sai ya
rinjayeshi.
Sannan Annabi sawya bawa Musulmi
wata Kariya daga Azabar Allah dake samun Alummatai na baya wadanda koda sunyi
imani in suka sabawa Allah da yin Shirka ko makamancinta sai ai musu azaba
kamar yadda akaiwa Banu Israila akasasu a dimuwar shekaru 40 nciki harda Annabi
Musa wanda anan dimuwar yai wafati, amma mu saboda alfarmar Annabi sai Allah
yai mana garantin in har Annabi saw na cikinmu to babu hanyar da zaai mana
Azaba inj kuma ya yi wafati to istigfarin day a koyar damu shi shine zai zamo
kariyar mu, to Jamaa in rahamar datafi wannan? Babu sam. Akwai bayanai da dama
da rashin lokaci bazi barni nai bayaninsu ba matukar ba gaba da gaba ake wannan
Jawabi ba.
2. Annabi Rahama ne Ga wanda ba Musulmi ba.
Su kuwa wadanda ba Musulmi ba in muka duba zamuga cewa
Annabi saw ya zame musu Rahama ta hanyar kasancewar ya basu aminci daga Azaba
da halakarwa, maana suma sunyi tarayya damu a cikin wannan amma su an kara musu
da wani abu wato shine duyk da kafircin su bazai musu azaba ta hanyar canja
musu Halittarsu zuwa BNirrai ko Alade ba kamar yadda akaiwa wasu Alummatai na
Bani Israi;la kamar Mutanen Garin Ailatu wadanda Allah yace dasu ku zamo Birrai
kaskantattu.
An tambayi Ibn Abbas gameda fadin Allah(وما
أرسلناك إلا رحمة للعالمين)
saiyace maanar wanna aya shine duk wanda yai imani da Allah da Ranar Lahira to
Allah ya bashi rahama ta Duniya da Lahira, wanda kuma bai Imani ba to an bashi
Aminci da lafiya daga Dukkan abinda aka yiwa alummatai da suka gabata na
kisfewa da jefewa. A wata riwayar kuma
wanda ya bi Annabi saw to zai samu wannan wanda bai bishi ba zai samu wannan
aminci.
A wani hadisi da Abu Hurairah ya karba daga Annabi kamar
yadda yazo a sahih Muslim an tambay Annabi saw cewa yayi Addua akan Mushrikai
sai yace aa bazanyi ba domin ni an aiko ni ne Rahama ga Talikai baki daya.
A lokacin da Annabi saw yaje Garin Ta’ifah don kiransu
zuwaga Allah amma suka jefeshi sukai masa raunuka jinni na zuba, Malaika
Jibrilu ya nemi Annabi saw ya bashi iznin jefa musu Duwatsu su talitse su amma
Annabi saw sai yace aa, Allah ka shirye su don basu sanni ba.
Ire iren wannan abubuwa bazasu Misaltu ba Arayuwar Shugaba
SAW sai dai mu takaita anan aakrshe mu cika da ishara ga Mamakon Ilmi da Annabi
saw ya kwararowa Halitta wanda shine yanzu Duniya ke takama dashi na Technology
da Likitanci, kowa ya sani Musulmi da suka Tarbiyyantu da Ilmin Annabi saw sune
suka watsa shi har Duniya take amfana, wannan ma wani maudu;I ne mai zaman
kansa. Da fatan Allah ya samu a rahamarsa saw.
3. Annabi Rahama ne Ga Halittu dab a yan Adam ba
Wadanda ba Mutane d Aljanu bama sun sami wannan Rahama ta
Annabi saw, wannan shima babine mai fadi, amma a gurguje mu kale shit a fuskar
yadda Annabi saw ya bada Tarbiyya wajen kare Hakkin Dabbobi da Tsirrai, Annabi saw ya nuna mana karshen Tausayi da
Rahama wajen yanka Dabbobi cewa kada a sake a wahal dasu, a yanka su da kaifin
wuka bad a gigarawa ba, sannan ya gaya mana a kan Dabba Allah ya shigar da wata
mata wuta data daure Magenta bata bata Ruwa ba, hakanan Manzo saw ya koyar damu
koda a lokutan yaki kada a cire tsirrai da Bishiyu.
Akwai hadisai da dama dake nuna yadda Annabi saw yake
tsawatarwa kan tsaurarawa Dabbobi. Annabi saw dai Rahama ce ga kowa ya zamo
ruwa mai game Duniya ko nace Ruwan Kan hanya in baka sha ba to lallai ka taka.
Da wadannan Kalmomi nawa nake cewa Allah ya maimaita mana
wannan munasaba muita ganinta cikin farin ciki, ya kuma Dulmiya mu cikin
Rahamar Annabi saw.
Comments
Post a Comment