**ME KA SANI GAMEDA DAREN NISF SH'ABAN?**

**ME KA SANI GAMEDA DAREN NISF SH'ABAN?**

Wannan dare Nada Tarihi da Muhimmanci a Musukinci, a cikin wannan dare ne na shekara ta biyu bayan Hijra Allah ya umarci Musulmi dasu canja Alkibla daga Baitil Makdisi zuwa Ka'aba bayan sun shafe watanni Goma sha shida suna fuskantar Baitil Makdisi Sallah inda take cewa:
قد نرى تقلب وجهك في السماء فلنولينك قبلة ترضىها، فول وجهك شطر المسجد الحرام، وحيث ما كنتم فولوا وجوهكم شطره.
Wanna dare Nada sunaye da dama fake nuna Muhimmancinsa ana kiransa:

Daren kubuta (ليلة البراءة)
Daren Addua (ليلة الدعا)
Daren Rabo (ليلة القسمة)
Daren amsawa(ليلة الإجابة)
Dare maj albarka (الليلة المباركة)
Daren Ceto (ليلة الشفاعة)
Daren Gafara da yantuwa daga Wuta(ليلة الغفران والعتق من النيران)
Wasu sunaeyn an samosu me daga Alkurani kamar
إنا أنزلنه في في ليلة مباركة إنا كنا منذرين فيها يفرق كل أمر حكيم
"Hakika mun saukar da Alkurani a **dare Mai albarka** hakika mu masu yi gargadi ne dashi (Alkurani) acikinsa (wannan dare) ake Rarrabe kowane lamari make hikma."

Wanna aya ta nuna mana cewa a wannandare be ake rarraba Al'amurra na Arziki da sauransu. Shine dalilin sunan Daren Rabo da Dare mai Albarka.

Annabi saw yana cewa:
«إن الله يطلع على عباده في ليلة النصف من شعبان، فيغفر للمؤمنين، ويملي للكافرين، ويدع أهل الحقد بحقدهم حتى يدعوه»
"Hakika Allah nayin tsinkaye akannbayin sa a Daren Nisf SH'ABAN said ya gafartawa Muminai Yakima jinkirawa Kafirai ya kyale ma'abota Kulli da kullin zuciyarsu har sai sun rokeshi" Imam Ahmad
A wani Hadisin Annabi saw yana cewa:
«من أحيا الليالي الخمس وجبت له الجنة ليلة التروية وليلة عرفة وليلة النحر وليلة الفطر وليلة النصف من شعبان» رواه إسماعيل الأصبهاني في "الترغيب والترهيب" من حديث معاذ بن جبل
"Wanda ya raya Darare Bihar Aljanna ta wajaba gareshi, Daren Tarwiyya, da Daren Arfa da Daren suka (8 da 9 da 10na Zulhijjati) da Daren Karamar Sallah, da Daren Nisfu SH'ABAN"

Imam Fakhruddin Razi yana fada a Tafsirinsa bayannyabkawo sabanin abinda aka nufi da LAILATIN MUBARAKATIN a ayar da muka kawo a baya, said yace:
"Ance wannan dare ankebanceshi da dabi'u guda Biyar sune:
1. Rarraba Lamurra masu hikma....(kamar Budget na shekara)
2. Falalar Ibada acikinta (said ya kawo wasu hadisai cikin haka)
3. Saukar Rahama saboda fading Annabi saw Allah yana jinkai daga Al'ummata da adadin Gashin Dabbobin Banu Kalb.
4. Tabbatar Rahma: Manzo saw yana cewa Allah yana gafartawa Baku day an Musulmi a wanna Dare banda Boka ko mai tsananin Husuma ko Mashayin Giya ko mai sabawa iyayensa ko mai dawwama akan yin Zina.
5. Allah ya bawa Annabi cikar Cetk cikin wannan dare, saboda ya roki Allah ceeton kaso 1/3 a Daren sha uku, aka bashi, ya roki kaso na 2/3 a Daren sha hudu aka bashi, sannan a Daren sha biyar (Nisfu SHA'ABAN) sai aka bashi ceton Al'umma baki dayansa saidai Wanda Allah ya koreshi iron korewar gujajjen Rakumi

**AYYUKA DA ADDUO'IN NISFU SHA'ABAN**
A dunkule anaso a yawaita Ibada da Zikirai da Karatun Alkurani a awanna dare, sanna anaso a azumci Ranar 15 ga watan, jamar yadda yazo. A wani Hadisi da Ibn Majah da Baihaki suka rawaitadaga Imamau Ali KRW inda. Annabi saw take cewa
«إذا كانت ليلة النصف من شعبان فقوموا ليلها وصوموا نهارها؛ فإن الله ينزل فيها لغروب الشمس إلى السماء الدنيا، فيقول: ألا من مستغفر فأغفر له، ألا مسترزق فأرزقه، ألا مبتلى فأعافيه، ألا كذا، ألا كذا، حتى يطلع الفجر» رواه محمد بن ماجة والبيهقي في شعب الإيمان.
"Idan Daren Nisfu Shaaban yazo Ku tsaida darensa Ku azumci Wuninsa Hakika Allah yana Tajalli a Saman Duniya a cikinta daga faduwar Rana sannannya kira: Akwai mainneman Gafara na gafarta masa? Akwai mai Neman Arziki na azurtashi? Akwai Wanda aka jarraba da bala'i na bashi lafiya?  Akwai mai kaza nai NASA kaza? Had dai zuwa hhudiwar Alfijir.

Bakiak Min sami addua da sirri daga Magabatan my na Tijaniya na Adduar nan Mashahuriya da akeyi hadeda Suratu Yasin kamar haka:

Da farko anason Karanta suratu Yaseeen Kafa Uku
1. Ta farko da Niyyar Allah ya bada tsawon Rayuwa
2. Ta biyu Da Niyyar Allah dauke Bala'i
3. Ta Ku da niyyar Neman Allah wadatar dakai daga abinda me hannun Jamaa.

Duk sadda ka karanta Yaseen kafa daya saika karanta wannan addua kafa Daya:

«اللَّهُمَّ يَا ذَا الْمَنِّ وَلَا يُمَنُّ عَلَيْهِ، يَا ذَا الْجَلَالِ وَالإِكْرَامِ، يَا ذَا الطَّوْلِ وَالإِنْعَامِ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ ظَهْرَ اللَّاجِئينَ، وَجَارَ الْمُسْتَجِيرِينَ، وَأَمَانَ الْخَائِفِينَ. اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ كَتَبْتَنِي عِنْدَكَ فِي أُمِّ الْكِتَابِ شَقِيًّا أَوْ مَحْرُومًا أَوْ مَطْرُودًا أَوْ مُقَتَّرًا عَلَيَّ فِي الرِّزْقِ، فَامْحُ اللَّهُمَّ بِفَضْلِكَ شَقَاوَتِي وَحِرْمَانِي وَطَرْدِي وَإِقْتَارَ رِزْقِي، وَأَثْبِتْنِي عِنْدَكَ فِي أُمِّ الْكِتَابِ سَعِيدًا مَرْزُوقًا مُوَفَّقًا لِلْخَيْرَاتِ، فَإِنَّكَ قُلْتَ وَقَوْلُكَ الْحَقُّ فِي كِتَابِكَ الْمُنَزَّلِ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّكَ الْمُرْسَلِ: ﴿يَمْحُو اللهُ مَا يَشَاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتَابِ﴾، إِلَهِي بِالتَّجَلِّي الْأَعْظَمِ فِي لَيْلَةِ النِّصْفِ مِنْ شَهْرِ شَعْبَانَ الْمُكَرَّمِ، الَّتِي يُفْرَقُ فِيهَا كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ وَيُبْرَمُ، أَنْ تَكْشِفَ عَنَّا مِنَ الْبَلَاءِ مَا نَعْلَمُ وَمَا لَا نَعْلَمُ وَمَا أَنْتَ بِهِ أَعْلَمُ، إِنَّكَ أَنْتَ الْأَعَزُّ الْأَكْرَمُ 
Sannan ka cike da Salatul Fatihi:

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى سيِّدِنَا محمدٍ ۞ الفاتِحِ لِمَا أُغْلِقَ ۞ ، والخَاتِمِ لِمَا سَبَقَ، ۞نَاصِرِ الحَقِّ بالحقِّ، ۞ والهادِي إلى صِرَاطِكَ الْمُسْتَقِيمِ۞، وَعَلَى آلِهِ حقَّ قَدْرِهِ ومِقْدَارِهِ العَظِيم ۞

Hakanan Akwai Sallah ta Nafila da ake yi wadda anaso mutun ya karanta Surat All Ikhlas wato Kulhuwallahu kafa dubu cikinta, Mutum ka iya yin Raka Coma fatiha da kulhuwa 100 a duk rakaa ko yayi adadin da zai dace dashi.

Allah ka datar damu ka bamu abinda mukai daidai kankarba ka yafe Wanda mukai kuskure.

Wasslamu Alaikum Dan Uwanku
Tahir Lawan Muaz Attijaneey

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY