الشيخ إبراهيم نياس يمدح الشيخ خليل الحصري وجمال عبد الناصر

Shehu Ibrahim yana Yabon Khalil Husari saboda yadda yake karanta Alakur'ani.

Labari ya inganta cewa Maulana Shehu Ibrahim Inyass shine ya baiwa shugaban Masar Jamal Abdunnasir Shawarar lallai a sanya Khalil Husari yai recording na saukar Alkurani a rika sanyawa a radion Masar kullum da safe da kuma yamma, hakan ta faru kuwa inda Husari yai saukar Alkurani aka fara sawa a gidajen radion Masar.
To  kamar yadda ake gani Wannan wata Takarda ce da Shehu RTA ya rubuta wasu baitoci da rubutun hannunsa kuma akan Letter head tasa a cikin wannan baitoci shehu na nuna jin dadin yadda Shugaban Masar ya sanya ake sanya Karatun Khalil Al Husari a gidan Radion Masar, wanda ya zamo Al'adar Shehu yake saurare a Madina Baye Kaulakha safe da yamma kullum.

Ga Baitocin:
١. صبوحي إذا أصبحت وهو غبوقي ** مرتل ذكر يزدري برحيق
٢. بكولخ يتلو الذكر وهو غيائب ** فتى النيل محمود الخليل صديقي
٣. كتاب لنا يبدي جمال جلاله ** به أرتجي نصري ونصر فريقي
٤. جزى الله باري الخلق جل جلاله ** جمالا جمالا سر كل صديقي
٥. عليكم بحبل الله قوم محمد ** أنار لأهل الخير خير طريقي.
Fassara
1. Abinda nake karin kumallo dashi in na wayi gari kullum kuma nake shansa da yammaci na, shine Ambato abin karantawa da dadinsa yake kaskantar da dadin Tuwan Raheeq.
2. Saurayin nan na Kogin Nilu kuma Abokina Khalil Husarishine yake karanta shi àbirnin Kaulaha amma abin mamaki shi baya nan a birnin.
3. Littafi ne wanda yake bayyana mana kyawun Jalalarsa, kuma da wannan littafi nake fatan samun taimakona dama taimakon Jamaata.
4.. Allah mahaliccin Halitta wanda girmansa ya buwaya ya sakawa Jamal da kyakykyawa, dama sirrin kowane Aboki.
5. Yaku Jamaar Annabi Muhammadu saw kui riko da wannan igiya ta Allah wanda shine yake haskaka hanyar Alheri ga ahlin alherin.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY