WAKAR KWAKI TA SHEHU ATIKU DA ALMAJIRINSA SHEIKH BALARABE JEGA


إعانةالشاكي بتاريخ كاكي
I'anatush shaki bi tarikh kwaki.
Shehi ya tsara wannan kasidane tare da Almajirinsa shekh Balarabe Haruna Jega kamar yadda zaa gani a karshe yana cewa:
  Fanai horo wurin Almajirina ** Yayo waka ta tarihi na kwaki.
Ya fara sai nazofa na taimaka mas ** Mukai waka I'anah du ga shaki
kuma yayitane sa'adda akayi wata yunwa a kasar Kano da kewaye, shekara ta 1361 HIJIRAH,Wajejen 1942.  sai shehi yake karkatar da mutane zuwa amfani da kwaki da kuma nuna musu hanyoyin sarrafashi saboda shi kwaki ba'a saba dashi ba sosai a kasar Hausa don abinci ne na mutanen kudancin NIGERIA. Mun sami wannan kasida da rubutun hannun Shehi Atiku da kuma rubutun hannun Shehu Balarabe Jega.
1.Fana fara da sunan Jalla sarki ** Tabaraka wanda shi yab bamu kwaki
2.Yasa mukazam musulmi jalla shine ** Ya aiko du ma'aaika mai saraki
3.Da tauhidi da addini kawimi ** Zuwa dukkan talakka har saraki 
4.Ilahal arshi mai kudura irada ** Alimun wahidun sarkin saraki
5.Fa shine yai halitta kullihinta ** Hakimun wanda yai doki da Jaki
6.Jamadun har Mala'ikku da jinnu ** Kazaka mutum da dukkan masu baki 
7.Abin ruwa ne fako nacikin kasane  ** Adan ikonsa yai kura da Zaki
8.Sannan ya bukatashemu mu duk ** Zuwa neamn abin sawa a baki
9.Fa dabbobi ciyawa anka basu ** Mutane ko ya bamu hadi da kwaki
10.Fa dabbobi ciyawa girman sarauta ** Muna dada godiya day a bamu kwaki
                ((HAKIKANINSA ) ((التعر يف به
11.Fashidai dan sarauta ne garinsu ** Adon haka bashi yawo shifa kwaki
12.Izan yaso fita kuma zashi yawo ** Fa sai izni fa yazo gun yan saraki
13.Suwo izni gareshi suwo  **
Shiga jirgi nufi nasa kunji kwaki 
                Fitowarsa daga garinsu  رحلته من بلاده
14.Da yayi nufin kano izini ya nema ** Ya hau jirgi yana sukuwassa kwaki
15.Yazo kano ya sauka wurin Akawu ** Acan atasha ya sauka kusan fa kwaki
16.Da Talakawa da masu kudin gari du  ** Suna tarbansa can a tasha fa kwaki
17.Zuwansa Kano kusan yaki yazo yi  ** Ya kawo taimako a garemu kwaki
18.Kazo nan zan gaya maka dan uwana ** Fa girman kai kadaina yiwa su rogo kwaki
19.Izan dai dukiya ce takamarka ** Fa Dantatan mu yai caffa ga kwaki  
20.Izan kuma dan saarauta takamarka ** Fa ga sarkin Kano ya san da kwaki
                         SAUKARSA A KANO نزوله في كنو
21.A zamani na Abdullahi yazzo ** Cikin birnin kano babban saraki 
22.Cikin hijra alif da dari da maitan ** Da sittin sai guda daya munga kwaki 
23.A zamani na Abbas yazzo fa amma ** Azamani na Usman babu kwaki  
24.Ya sauka tasha yana khudba fa kullum ** Kuzo ku gareni nine rogo kwaki
25.Mutane sun rijif sunje gareshi  **  Suna caffa suna gaisheshi kwaki
26.Da dattijai da yara yan kanana ** Da yan mata da masu zama a jaki
27.Inyamuri har samari manya-manya ** Anan a kano suna ladabi ga kwaki
28.Mutan Sabon gari da Fagge na gansu ** Suna rurubi wurin gaisar da kwaki.
Zamu cigaba...

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY