Manahilur Rashad na Sheikh Abubakar Atiq (25)



Amsar tambaya ta 25


Magana akan Gausi ko ina yake yanzu ba aikin mu bane, kuma jahiltarmu da hakan bazi cutar damu ba abinda ake nema daga garemu dama dukkan kowa shine mu mika wuya da gasgastawa ga duk wanda akce dakai Gausi ne, Jahiltarsa da ainahinsa bazai cutar dakai baduk sadda ka kudurce a zuciyarka cewa shine Gausun, koda baka sanshi ba, abinda zai cutar sakai shine rashin mika wuya koda kuwa a cikin gidanka yake.
Abinda yake lazimcewa mai gasgatawa da kebance kebancen waliyyai shine ya toshe kunnuwansa daga sauraren dukkan sukan masu suka, ya runtse idonsa daga barin kallon aibin dukkan musulmi, da kame harshensa ga barin kirkirar zance ga wani daga yan uwansa Musulmi, a cikin hakanne tsira daga tabewa take da rabauta da dukkan kyautayi.
Wannan shine abinda na kudurce kuma nake Addini nag a Allah akansa. Wassalam.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY