WAKAR KWAKI TA SHEIKH ATIKU DA SHEIKH BALARABE JEGA 2

HALAYENSA DA DABI'UNSA أحواله وطبائعه

Fa shidai walla saukin kai gareshi
Fa baya ja da kowa kunji kwaki

Fa domin ko talakka sayo ya cishi
Da sauki zaya cishi halinsa kwaki

Akan samai ruwa fa kadan a cishi
Ana ma hanfudashi kadai a baki

Izan kuwa anka so wahala gareshi
Fa sai yazamo abincin yan saraki

Akan teba dashi da miya ta kwanbo
Da man shanu da nama kanci kwaki

Akwai ajabi cikin gari na rogo
Abincin yan mutanan yamma kwaki [1]

Fa yayi musharaka da hadin kasammu
Kamar Gero da Dawa harda Wakei

Kazalika harda shinkafa hakannan
Kamad da Alkama Doya yi kwaki

Ana waina da Alkaki dashi har
Akanyi Wasa-wasa dana rogo kwaki [2]

Izan an rafka taushe ankasa Mai
Da nama ya zamo sai yan saraki

Izan anso fura nono akan sa
Adama ko da sukkar anci kwaki

Akanyi Tuwo dashi a gama da Gari
A tuke sai taci da Miya fa kwaki

Akanyi tuwo na shinkafa a tuke
Asa taushe fasai shagali da kwaki

Ana Dambu dashi a gama da Ganye
Akwai shi da martabobi rogo kwaki

Ya kanyi fushi izan an bata ransa
Barin ladabi  ka motsa fushin saraki

Idan ka jikashi tun baka dakata ba
Ya kumbura wanga shi ka fusata kwaki

Izan ka shashi lallai zaiyi illah
Cikin ciki sai ya kumbura yai na Jaki

Su kwaki ai saraki ne hakika
Fa wake yin irin mulkinsa kwaki ?

Adon hakanan da zamaninsa yazzo
Faba motsi gurin sauran saraki

Su Gero sun fake hakanan su Dawa
Adan sababin zuwan Babansu kwaki

Su Wake ba mujin motsinsu su du
Su Masra sun fake sun tsorci kwaki

Su Rogo su Dankali duk sunka buya
Faba'a ganinsu don tsoronsa kwaki

Su Zogale sai ka barsu makaryata ne
Su Tafasa du kazam ladabi ga kwaki

Rama ma tayi karya tun a bara
Adan haka sai ta buya da taji kwaki

Sarautar tasa ba Kadhi da Joji
Adon yaki yazo shi Rogo kwak [3]i

Walakin dai akwai ofis gareshi
Cikin kwano yake mulkinsa kwaki

Kuli-kuli shi kadai ya tsayawa daga
Gurin sarkinsa shine madawaki

Izan an nemi sulke sai fa mansa
Akan yafa su gishirine Dawaki

Su Barkono kusan sune mabusa
Gurin yaki sukan zuga rogo kwaki

Takobi cokaline babu shakka
Da yatsu ne kibobin Rogo kwaki

Idan damarunsa dun a yaki
Nufinsa shigi cikin kofa ta baki

Izan akasa ruwa bayan hakannan
Fa bom kenan na Garin Rogo Kwaki




[1] . mutanan yamma = yana yarabawa mutan yamma maso kudancin Nigeria
[2]. wasa-wasa = waina ce da akeyi da rogo, ko gero ko wake.
[3] - kadi = Alkali joji= shugaban Alkalai

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY