Waye farkon Wanda ya fara Sawa Kaaba Riga?
Waye farkon Wanda ya fara Sawa Kaaba Riga? Mahmil kenan Na samu Labarin cewa an sa wani Malami A Radio Rahma dake KANO da yai Daawar cewa wai Tufatar da Kaaba da akeyi Al'ada ce bata daga addini abune da Turkawa sukayi zamaninsu shine aka dore a haka. To BA haka abin hake BA, tufafin Kaaba Sunnah CE Ta Annabi saw. Farkon Wanda ya sawa Kaaba riga? Galibin abinda akafi tafiya akai shine Sarkin Himyar Ta Kasar Yemen Tubbaul Yamani Wanda yai Mulki shekaru 378 zuwa 420 Miladiyya wato kan a haifi Annabi saw da Sama da shekaru 150 Kenan shine Wanda ya Fara sanyawa Kaaba Riga sadda hanya ya biyo dashi Malamai suka gaya masa cewa Makka be Mahaifar Annabi saw don haka ya yiwa Kaaba riga yayi Mata mukulli ya Sanya ai Mata turare. Wata riwayar kuma na ance Annabi Ismail ne Amma hakan Mai Rauni ne. Tun daga Kansa kuma ake yimata Riga duk da cewa BA wani Launi no tsayayyen yafi da ake Sanya Mata. Bayan Fathu Makka kuma Annabi saw ya kyale irin tufafin da ake Mata Hari Saida wat...