#Basasa
Duk Wanda yaji wannan Kalmar yasan ana maganar Yaki ne, kuma an fara amfani da itane a harshenbHausa a Zamanin da akai yakin Basasar Kano Zamanin Sarkin Kano Tukur a shekarar 1894 Inda yakin ya kai ga juyin mulki da Kashe Sarki Tukur a Hannun Yusufawa da Dora Sarki. Kano Aliyu (ALU) a karagar mulkin Kano.
Shin ko kunsan Menene asalin Kalmar Basasa a Hausa?
Kamar yadda wani manazarci ya fada mai suna A.M. Fika (1978) a cikin wani littafinsa mai suna The Kano civil war and British over rule 1882-1940.  Wanan Kalmar ta samo asali ne daga tarihin shekarar hijra da akai wannan yaki cikinta wato 1312 AH. Duk da cewa an yiwa Kalmar gyaran fuska ya nuna cewa in aka karanto haruffan hisabi Kamar haka:
باسش
١٣١٢
Wato Ba2, A1, Sa300, Sha100 
Said aka shafe digo uku na shinun suka koma Sa kawai.

Nace: hakan na iya kasancewa Duk da akwai duba cikin hakan, amma me yiwuwane duba da irin yadda malamanmu suke amfani da Kalmomin hisabi don Nuna shekarar da wani Abu ya faru ko shekarar da sukai waka ko talifi, ko adadin baitocin waka Kamar yadda Shehu Atiku take yawan yi a kasidunsa na Hausa da Larabci.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY