Cikakken Mawaki Shareef Alhaji Rabiu Usman Baba


Cikakken Mawaki
Shareef Alhaji Rabiu Usman Baba

A safiyar yau dinnan muka tashi da labarin rasuwar mawakin Annabi saw sharif Rabiu Usman Baba wanda haifaffen Unguwar Gabari ne dake cikin Birnin Kano a wajejen 1965 kuma ya tashi anan kafin su koma unguwar Gwammaja inda ya kafa kamfainsa na nadar wakokin yabo, a karshe ya koma Unguwar Jan Bulo dake titin Rijiyar Zaki inda ya rasu a nan.
Sunan Marigayi Rabiu zai wanzu Shekaru barkatai nan gaba saboda yadda sautinsa ya zaga dukkan wani sako da harshen Hausa ya isa a duniya.
Na zabi na kira wannan mawaki da cikakken mawaki ne saboda yadda Allah yah ore masa waken Yabo ko nace Bege kamar yadda masu nazarin Hausa suke kiran wannan fanni. A iya sanina Malam Rabiu Shine mawaki daya tilo tsakanin mawakan Bege na Hausa da yazamo wakarsa ta shafo duk wani bangare  ko nace jigo na waka a addininin Musulunci. Tun daga wakokin tauhidi da tsarkake Allah zuwa begen Annabi SAW Sahabbansa Ahlin Gidansa  Matayensa iyayensa masu shayar dashi Waliyyai da Shehunnani na mabambamtan Dariku, Yabon Shehu Tijjani Da Shehu Ibrahim Inyass kai harda wakokin munasabobi kamar Taziyya Aure Maulidi Haihuwa da ma wakar SO wadda muka fi sani a larabci da Gazal har zambo ma baa barshi a baya bay a zamo yakan bulala ga makiya Annabi saw ko masu tauye darajarsa.
A fannin yabon Allah saw zamuga yadda Malam Rabiu ya zamo yak ware wajen kadaita Allah, a duk farkon wakarsa sai ya sanya yabo ga Allah kafin faraway, misali mudauki mukaddamar wakarsa ta Sadiya yana cewa:
Da sunaka faraka baitoci
Sarkin dayayi masassaki yaiyi kotoci
Allah sarhin rahamane da adalci
Masu sabo nasa ma yana basu sai sunci
Dan ko sabonsu bazaya tauyeshi komai ba.
A wannan baiti daya zaka gane kwarewarsa a wannan fanni ta yadda yake kawo ayoyi da hadisai ya kunshe su a baitukansa, don a wannan baiti zamuga yadda Malam Rabiu Usman Baba ya kawo fadin Allah cikin hadisi Kudsi:
يا عبادي لو أن أولكم وآخركم وإنسكم وجنكم كانوا على أفجر قلب رجل واحد منكم ما نقص ذلك من ملكي شيئا
Maana; yaku bayina da dai cewa na farkonku dana karshenku da Mutanenku da Aljaninku zasu zamo a bisa zuciyar mafi fajirci daga cikinku to wannan bazai tauye komai daga mulkina ba.

Kuma zamuga a yan shekarunnan yadda ya fidda waka ta yabon Allah mai taken BABU TANTAMA wadda amshinta na nuna yabon Annabi saw ce amma a haqiqa yaboce ga Allah.
Akwai wasu wakoki da suke kamar na sufanci irinsu Tantama da Raddin Tantama din, wadanda a iya sanyasu a waken yabon Allah swt
 Idan muka dauki yabon Shugaba SAW zamuga yadda Malam Rabiu ya fara tashe tun a shekarun 1980s inda yazamo mawakin Tijjaniya daya mamaye fagen yabon Annabi da Hausa kuma malakarsa ta iya yin waka bata taba mutuwa ba har ya koma ga Allah a wannan shekara yayi wakoki da shuhurarsu ta keta Duniya kamar wakarsa data fito dashi wato TSUMAGIYA wanda wannan suna yazamo sunan kamfanin Malam Rabiu Usman Baba na faidda wakoki wato TUSMAGIYA ISLAMIC STUDIO. Kana wakokinsa na wancan lokaci irinsu Zuma Shayabo Salka da sauransu.
Sahabbai da matayen Annabi saw kuwa malam Rabiu ya wakesu da wakoki mabambanta daga ciki wakarsa da tazamo kamar silsila ce daya wake matayen Annabi saw ya kawo darajojinsu da wakarsa day a hade sahabbai goma da akiwa bushara da Aljanna.
Abin shaawa shine yadda wakarsa ta HALIMATUS SADIYA da ya wake mai shayar da Annabi saw ta zamo kundi na tarihin haihuwar Annabi saw da shayar dashi cikin salo mai jan hankali, wadda a jere aka shekara uku ana bashi kyautar wakar datai fice a tsakanin mawakan Annabi saw.
Ahlil baiti kuwa ma iya cewa a mawakan hausa shine ya fara wakesu da wakarsa mai taken AHLI BAITI ko muce INA SON KU SHARIFAI, sannan mawaka suka biyo masa baya cikin haka.
A fagen Shehunai kuwa ya yabi manyan waliyyai da sukai shuhura tun daga Sidi Abdul kadir Jilani Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim rta wanda wakarsa ta Sharifiya da yaiwa Shehu Tijani tazamo gagara badau har yau dinnan. Dama kam wakokin yabon Gausi baa cewa komai bai zamo yana waka sai ya yabeshi banda wakoki da yayi na yabonsa tun a shekarun 1990s da wakarsa ta Shehu Barhama kaulahi.
Wakokin munasaba kuwa wato wakar da mawaka keyi saboda faruwar wani abu Sharif Rabiu yayisu ba adadi, tun daga kan maraba da Maulidi, Taaziyyar mutane kamar mawaki Malam Rufai da jimamin faduwar Jirgin sama a Gwammaja da taaziyar wadanda suka mutu a cikinsa. Hakanan akwai urnar Aure da mawakan suka rikayi a junansu musamman a karshen shekarun 1980s zuwa farkon 1990s.
Bugu da kari akwai kaasidun da zamu kirasu na Taammuli da nazarin rayuwa kamar wakokinsa biyu da yayi kan Mutuwa wato WAYYO KAINA MUTUWA IGACE BATA FITA da kuma WAYYO NI WAYO NI MUTUWA BATA KYALE KOWABA.
KIRKIRE KIRKIEN RABIU USMAN BABA A FAGEN WAKA
Daga abinda bazaar manta da Rabiu ba a fagen waka shine kasancewarsa na farko cikin wadanda suka far amafani da Mandiri a wakar bege musamman a tsakankanin Tijjanawa, wanda zamantakewarsu da Kadirawa tasa Rabiu ya aro bugun mandiri sauran mawaka na Tijjaniya suka karba bayan doguwar muhawara tun shekarun 1980s. sannan a duk mawakan yabon Annabi saw na Hausa sun san amfani ne da kayan kidan zamani na Piano ta hannun Malam Rabiu Usman Baba a lokacin day a fara amfani dasu a wakarsa ta yabon Annabi saw RABBIY RABBIY wanda a lokacin da ya fitar da wannan waka an samu cece kuce mai tsanani a Kano inda mutane suke ganin malam Rabiu yazo da wasa a yabon Annabi saw, a karshe Rabiu yayi waka da yake bada uzurin cewa baiyi don wasa ba inda yake cewa:
Ya Allah ganar da Bayinka
Rabiu Usman Baba bai nufi wasa ba.
A karshe zamuga cewa Allah ya amsa wanna addua kuma ya duba kyawun zuciyarsa ya zamo kowane mawaki ya koma amfani da wadanna kaya a karshe ma dai ya zamo shugaban kungiyar mawakan yabon Annabi saw ta kasa baki daya wato SHUARA’UL ISLAM wadda ya rike har komawarsa ga Allah.
Yawan wakokinsa da karfin haddarsa
Abune mai whala a iya gane wakokin malam Rabiu saboda yadda ya gabata munc Sharif ya fara waka tun yanada kuruciyarsa kuma ba kamar sauran mawaka da baiwarsu take sama tai kasa ko ta mace na shekaru baa ji duriyarsa ko sabuwar wakar sa ba, aa shi  Malam Rabiu ta zamo tsawon shekaru kusan Arabain da yayi yana bege baiwar wakarsa da kyawunta sun zamo a kunne kodayaushe, kowane lokaci kadan ya shude zakaji sabuwar waka kuma bazakace waka mai raunin jigo ko fasaha ba. Shiyasa adadin zai wuya a iya fadinsa.
Gajeren takadiri gameda adadin wakokinsa shine na sami labara cewa an taba gayyatarsa majlisi a garin Jos farkon shekarun 2000s inda ya shafe awa 24 tas yana karanto wakokinsa ba tareda maimaici ba sai dai a tsaya ai sallah ko ai abinci. Wannan ne yasa ni nake ganin tabbas malam Rabiu ya zamo ya risku da sahun maakan Duniya irinsu Muhammadu Rafi na kasar India, don tabbas Malam Rabiu ya kasance mausuah wato abinda bature ke kira encyclopedia maana Kundi ne Babba cikin fagen wakar Bege a karni na 21.

CIKAWA
Hakika in mukai duban tsanaki ga rayuwa da wakokin Sharif Rabiu Usaman Baba zamuce eh ya cancanta mu kirashi Cikakken Mawaki da yayi tasiri da waninsa baiyi ba  akasar Hausa cikin fagen wakokin yabo maza da mata malamai da ammawa da masu kudi da yara da manya sun tasirantu kwarai da wakokinsa, hakanan wakokinsa sun zamo kamar tunziri ne mai tashin tsimin kaunar Maaiki a zukatan Masoyan Annabi saw. Sannan muna kira gay an uwanm masu rubutu akan yanar gizo da mu hada karfi wajen rubuta tarihin mawakanmu da malamanmu a kan yanar gizo musamman a shafinnan mai farin jinni na Wikipedia cikin yarukan Hausa Turanci da Larabci don duniya tasan dasu da gudunmowarsu a fagen da suka kware a ciki.
Dafatan Allah yajikan Shareef Rabiu Usman Baba ya jikanmu bayansa.
Wassalam
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
09 May 2019
04 RAMADAN 1440

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY