Wasikar ga yan Hakika

wannan ita ce wasikar da Shehul-Islam, Alh. Ibrahim Inyass ya rubuto da rubutun hannunsa mai albarka, kuma akan letter-heading ta sa.

Shehu ya rubuto wannan wasika ne akan mutumin da ya fara watsa irin wadannan munanan aqidu , shi ne : ABDULLAHI JAFARU. Da kuma wani mutum irinsa mai suna JIBRIL.

Ga fassarata nan da hausa don nuna kubutar Shehu

 Kamar yadda zaku gani Maulanmu ya rubuta wannan wasika ranar 8 ga Ramadan shekara ta 1380 A.H.

 Ya fara da cewa:

DUKKANIN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH.
ASSALAMU ALAIKUM YA SAHABBANMU, MASOYANMU, MASU TAIMAKON ADDINI DA DARIKA.
 BAYAN NA AIKO MUKU DA WASIKAR FARKO SAI KUMA NA SAMI LABARIN ABDULLAHI JA'AFARU WANDA SAUDA YAWA NA YI TA KOKARIN SHIRYAR DA SHI ZUWA DAIDAI AMMA YAKI, SAI DAI BIN SON RANSA, DA SHAIDANINSA, DA DUNIYARSA, DA SON ZUCIYARSA. MAI YIWUWA ALLAH NE YA KE NUFINSA DA RASHIN ARZIKI. DON HAKA, NA DAUKEMASA IZINI (izinin bada darika da tarbiyya), SHI KUMA JIBRILU IDAN YA NA NEMAN ALKHAIRI KUMA YA NA SON YA CIGABA DA ABUTARMU TO YA ABOCI MANYAN SAHABBANMU, YA BI TAFARKINSU. ADDINI DAI NA ALLAH NE, BA A RIKO DA SHI DON WASA, KO DON CINIKI (ci da addini), KO DON SHA'AWA, SHI DAI BABBAN JIHADI NE DA KARAMIN JIHADI (Yakin daukaka addini da yaki da zuciya), DUk ABINDA BA HAKA BA KUWA TO HANYAR SHAIDAN NE, IDAN KUMA SHIMA WANNAN MUTUM BA ZAI KARBI WANNAN ABU DA NA FADA BA TO KU JUYAR DA SHI DAGA CIKINKU SHIMA NA DAUKE MASA IZINI NA BARSHI YAJE SHI DA RANSA.

 KU HUTA LAFIYA,
 IBRAHIM DAN ABDULLAHI ALKOULKHIY.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY