ZIYARAR GWAMNA GANDUJE EGYPT NA SON BUDE RESHEN JAMIAR MANSURA TA EGYPT A KANO
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yakai wata Ziyara a zuwa Jamiar Mansurah dake kasar Masar wato Egypt Ranar Litinin 7 ga Nuwambar nban da zummar ganin wannan Jamia ta kafa reshenta a Jihar Kano.
Shugaban Jamiar ta Mansura Professor Muhammad Al KQanawy ne ya tarbi Gwamnan da ya sami rakiyar shugaban Dr Hafsatu Gandje da Jakadan Nigeria a Kasar ta Masar Mal Muhammad Abdulkadir, sai Shugabar Hukumar bada Tallafin karatu ta Kano Dr Fatima Umar sai Dr Salihu Tanko da sauransu.
Gwamna Ganduje ya godewa Sashin Jinya na Jamiar da ya yiwa wani dan Kano Aiki bayan fadowarsa daga Benen dakin Kwanansa sannan ya godewa Jamiar Bisa lura da yan Nigeria dake Makarantar.
a wani cigaban kuma Gwamnan ya nemi Jamiar data bude Bangarenta a Kano ta yadda Gwamnatinsa zata bada wuri da duka kayan da ake bukata yayinda Jamiar ta MANSURAH zata samar da Jamianta da kuma kwararrun malamai da zasu horar da Malamai na Kano daga doguwar gogewar da suke da ita ta fannin aikin Jamia.
Comments
Post a Comment