WAFATIN ANNABI SAW 16

TSOHON HOTON SAKIFATBANI SA'IDATA INDA AKAIWA S ABUBAKAR MUBAYAA


KHILAFA:

ZABEN ABUBAKAR (RTA) A MATSAYIN KHALIFAN Manzo (SAW):
Anan nakeso na dan dawo damu baya kadan ma'ana kafin binne Manzo (SAW).
Lokacin da Manzo (SAW) yayi wafati sai mutannen Madina suka taru a wani wuri da ake kira (Sakiifatu bani Sa'udata).
MECECE SAKIFATU BANI SA'IDAH:
Sakifa dai wani wuri ne mai inuwa da girma, kusa da kasuwar Madina, kuma tana wajen kasar Kabilar bani Sa'adah, waje ne da su Ansar (Aus da Khazraj) suka saba taruwa a wurin domin yin shawarwari da yanke lamuransu na yau da kullum, kamar yadda Darun Nadwa yake ga ahlin Makka.
Sa'adda labarin wafatin Manzo (SAW) ya bazu a Madina sai su Ansaru suka taru a wannan wuri domin su nada Khalifa a tsakaninsu, su kuma S. Ali da Abbasu da Zubair binil Auwam da Dalhatu bn Ubaidillahi sai suka tare a gidan Sayyada fadima, sauran Muhajirun suka koma kusa da Abubakar da Umar, ana haka sai wani mutum daga Ansar yazo ya sami S. Abubakar yace dashi "ga kabilun can na Ansaru sun taru a Sakifat bani Sa’idah tare da Sa'adu Bin Ubbadata don zabar shugaba in kuna da bukata cikin lamarin mutane to ku riskesu tun kafin lamarinsu yayi girma".
Daga nan sai S. Umar yace da Abubakar zo mu tafi izuwa 'yan uwanmu na Ansaru muga abin da suke ciki, nan da nan suka tafi akan hanyarsu suka hadu da Abu Ubaidah Amiru binil Jarrah, suka rankaya tare.
Da isarsu sai suka tarar wani daga Ansar ya tashi yana magana a cikinsu, yana cewa:- "…..mune Ansarullahi kuma rundunar Musulunci, ku Muhajiruna jama'ace daga cikin mu jama'a daga cikin ku sun taho daga kauye zuwa birni, sunaso su turemu daga Asalinmu su kwace mana lamari.
Daga nan sai S. Umar yai yunkurin magana, amma sai Abubakar yace dan saurara, sai ya fara magana yana mai cewa "yaku jama'ar Ansaru duk abin da kuke fada na falala, dake wajenku ta karbar musulunci da saukar masu hijira haka take, to amma kunsani larabawa basa bin kowace kabila cikin shu'unai sai dai kuraish…., saboda haka ku zamo mana wazirai mu kuma mu zamo sarakuna, baza ayi wani lamari ko yanke shawara ba sai daku.
S. Abubakar bai gama maganarsa ba sai wani Sahabi mai suna Habbabu binil Munzir ya tashi yace:- "a'a sai dai kuzamo wazirai mu kuma mu kuma sarakuna, sai Abubakar yace ai wannan lamari bazai yiwa ba sai da wannan kabila ta kuraishu, sai Habbabu yace:- "yaku taron Ansaru ku rike lamarinku domin mutane nan – wato Muhajirun – suna cikin kasa-karkashin inuwarku, saboda haka babu wani mai tsaurin idon da zai zo yayi taka haye ga halifancinku ……, sabida haka sai dai ya zamo akwai khalifa a cikin mu – Ansaru – kuma da khalifa a cikin ku – Muhajirrun, sai S. Umar yace sam bazai yuwuba, fa taba ganin inda akayi sarki biyu akan daula daya ba?
Haka dai bayan dogon cece kuce S. Abubakar ya kama hannun S. Umar da Abu Ubaidah yace "na yarje muku dayan mutanennan duk wanda kuka yiwa mubaya'a yayi".
Nan da nan sai S. Umar yace:- "haka baza ta yiwu ba, alhali gaka araye, ai bazan jinkirta da kai ba bisa matsayin da Manzo (SAW) ya dora kaba, kuma ai laifi ne ni gareni na shugabanci jama'ar da Abubakar yake cikinsu, saboda haka shimfida hannunka nai maka mubaya'a, sai S. Umar ya kama hannun S. Abubakar yai masa mubaya'a, mutane kowa yazo yai masa mbaya'a, ya zama khalifan Manzo (SAW).
Daga bisani S. Abubakar (RTA) ya dawo masallacin Manzo (SAW) inda sauran Musulmi sukayi masa mubaya'a ya zamo khalifa Annabi (SAW).
(KHUDBAR S. ABUBAKAR):
Bayan da mubayarsa ta tabbata sai ya hau mimbari yayi khudbarsa shahararriya wadda yake cewa bayan godiya ga Allah da salati:
"Yaku mutane, hakika ni an shugabantar da ni a kanku, alhali ni ba nine mafificinku ba, inda na kyautata to ku taimakamin, in na kauce ku katartar dani,.. Rarrauna a cikin ku mai karfi ne a wurina har sai na karbo masa hakkiknsa, mai karfi a cikin ku kuma rarrauna ne har sai na karbo hakki daga gareshi, kada dayan ku yabar jihadi domin shi (Jihadi) mutane basu barshi ba sai Allah ya bugesu da kaskanci, kuyi min biyayya matukar nabi Allah a cikin ku, idan na saba masa to babu biyayya a gareni akanku, ku tashi izuwa sallah Allah yaji kanku".

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY