RADDI GA DR JALO: IYAYEN ANNABI SAW BA YAN WUTA BANE



WANNAN HOTON ANA CEWA NAN NE KABARIN S. AMINATU

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.
A satin day a gabata wani dan uwa ya kirawo niyana mai nuna min damuwarsa gameda wani Rubutu da Dr Jalo Jalingoya wallafa a shafinsa na Facebook wanda yatabo iyayen Annabi saw a ciki yana mai nanata cewa lallai su yan wuta ne, hakan ya daga masa hankali yana cewa ai masa raddi saboda kada Jamaa su rudu da wannan rubutu nasa.
DALILN DR JALO A HADISI;
Masu wannan akida suna Dogaro ne da wani Hadisi da Muslim ya rawaito a sahihinsa daga Anas rta yace wani mutum yazo wajen Annabio saw ya tambayeshi INA BABANA? Samanzo sawyace dashi “YANA WUTA” lokacion day a juya sai Manzo sawya kirawoshi yace dashi “BABANA DA NAKA SUNA WUTA”
RADDI
To wannan Raddi zai zamo a takaici don kuwa tuni Malamai sunyi rubuce rubuce sun kasha mas’alar: Jalaluddin Suyudi Littafi guda shida shi kadai ya rubuta kan Allah wdai ga masu wannan Magana haka duk wani wanda akasan ya isa a Duniyar Ilmi ya tabbatar da cewa mai fadar wannan mgana kan iyayen Annbi saw to yana da matsala a zuciyarsa, sunyi talifai da dama da sunayensu kawai ya isa raddi ga mai inkari dafga wadannan Malamai bar na ambaci kadan:
Imamu Fakrur Arrazi, Imam Ibn Arabi Almaliki, Alhafiz Al Kurdubi. Sibd Ibnil Jauziy. Imam Al Alusi. Ibn Shahin. Alhafiz Shamsuddin Addimashqy. Sarkin masu hadisi Ibn Hajar Al Asqalani. Imam Alqasdalaniy imam Azzarqani da makamantansu.
HADISIN MUSLIM YACI KARO DA ALKURANI
1.: Wannan Hadisi kamar yadda muka fada a baya MULIM ne ya rawaice shi a sahihinsa, amma abinda zamu fara sanyawa a gaba shine musan shin menene abinda ake gabatarwa a wajen kafa hujja a addinin Musulunci?
Naam, dole ne a fara gabatar da Alkurani akan Hadisi duk ingancin hadisi kuwa, shi yasa da farko wannan Hadisi dole mu bijirar dashi ga Alkur’ani wanda in mukai hakan zamuga yaci karo da ayar  Alkur’ani a fili wadda allah yake cewa:
وما كنا مععذبين حتى نبعث رسولا
 Maana “Bamu zamo masu yin azaba (ga wani ko wata) ba har sai mun aiko Manzo).
Dafadinsa:
لتنذر قوما ما أنذر آباءهم فهم غفلون
Bisa doron wannan ayOYI da wacce hujja zaa kama iyayen Annabi saw har ai musu Azaba in ma mun kaddara cewa sun bautawa Gumaka? Babu!
A kaidar Malamai na musulunci kaf dinsu sun hadu akan cewa idan Hadisi wanda shi labarin AAHAADI NE wato labarin da mutum daya ko makamancisa ya rawito_ yaci karo da ayar Alkurani wanda shi riwayarsa MUTAWATIRA ce wadda take mai yankakken tabbas ne, kuma babu wata kafa da zaa iya hadasu wuri guda to dole a bar wannan hadisi ko in ba makawa ai masa Tawili.
Shima tawilin yanada tasa matsalar misali a wannan Hadisi wasu sun yi masa Tawilin cewa kalamr ABIY wato BABANA tana Nufin Baffansa Ab Dalib wanda wannan ma akwai Magana da cewa malama da damai basu yarda da cewa Abu Dalib yana wuta ba, wasu kuma na ganin ai Tawilinsa da Abu Lahabin wanda Alkurani ya tabbatar da Nassi cewa dan Wuta ne.
In har ya zamo yaya mata da aka binne su A Jahiliyya Allah zai musu Adalci da tayar dasu a tambayi cewa da wane Zunubin aka binne su da ransu mai zaisa kuma a ce iyayen Annabi saw suna wuta! Hakanan kuma Allah swt yana Tabbatarwa cewa bai aiko manzo ga Ahlin Makkah ba kafin zuwan Annabi saw da fadinsa
وما أرسلنا إليهم قبلك من نذير
Banda wadannan akwai wasu ayoyi da daman gaske da suke nuna cewa Allah baya halakar da mutane haka siddan ba tare day a aiko manzo sun ki binsa ba.
ILLAR DAKE CIKIN HADISIN “BABANA DA NAKA SUNA WUTA”
2. In muka dawo kan Ingancin Hadisin kansa zamuga cewa an sameshi ta hanya ingatacciya amma kuma malamai sun gano wata illah a cikinsa guda biyu
a. illah ta farko malaman hadisi sun rawaito wannan hadisi ta fuskoki daban daban amma a cikin tasu riwayar babu fadin   “BABANA DA NAKA SUNA WUTA” bari aabinda yake wadancan riwayoyi shine “DUK YADDA KAGA KABARIN KAFIRI KAI MASA BUSHARA DA WUTA” Ibn Majah ya rawitoshi a hadisi na 1573 hakanan Dabarani da Bazzaru da Baihaki.
Donhaka kodan Ladab ga Annabi saw ya zama wajibi a ajiye wancan Hadisi a dauki wadannan masu lafazin “DUK YADDA KAGA KABARIN KAFIRI KAI MASA BUSHARA DA WUTA”
b. illah ta biyu itace shi wanda ya rawaici hadisin shine HAMMADU BN SALAMAH daga Sabit wadda a cikinta aka samu wannan lafazi na kai iayen Annabi as wuta, shi kuwa HAMMADU BN SALAMAH an tabbatar cewa a karshe daya fara tsufa Haddarsa ta raunana saboda haka aka samu MUNKARAI a hadisansa. kuma yana da wani agola da aka tabbatar yana cusa masa maganganu a hadisan day a rubuta batare day a sani ba, kuma saboda wannan rauni na hadda baya ganewa.
Akwai wata hanyar ta biyu daga MAAMAR daga sabit itama wannan riwaya babu lafazin kai iyayen Annabi saw wuta,
Akwai wata hanyar itama ta uku daga Ibrahim bn Saad daga Ibn Shihab Azzuhri hark an saad bn Abi waqqas shima tazzo ne babu wancan lafazi “babana da babanka na wuta” bari tazo da “inka shude da kabarin kafiri kai masa bushara da wuta”
3. Daga Sunna akwai wasu hadisai dake nuna girma da darajar tsatson Annabi saw kuma suke nuna cewa ba wanda ya zamo dan wuta a cikin Kakanninsa kaf daga wadannan hadisai zamu ambaci:
NA DAYA: Muslim ya rawaita daga Wasilat bn Asqa’I yace naji Annabi saw yana cewaAllah ya zabi Kabilar KINANATU  daga yayan Isma’il ya zabi Quraiyshu daga KINANATA ya zabi Bani HASHIM daga QURAYSH ni kuma ya zabeni daga bani Hashi.” Wannan Hadisi basai an fasa shi ba an gane irin zabin da akayi bata yiwo a zabi mutum ba tare da an yanta shi  ba
NA BIYU Abu Naim ya rawaita cewa Annabi saw yana cewa “ALLAH BAI GUSHE BA YANA CIRO NI DAGA TSATSON MAZA MASU TSARKI ZUWA MAHAIFUN IYAYE MATA MASU TSARKI HAR YA FITAR DANI ABIN TSARKAKEWA, WATA JAMAA BIYU BATA RABU BA SAI NA ZAMO CIKIN WADDA TAFI ALHERI”
Mu takaita anan mu kawo dalilai na hankali kuma
DALILAI NA HANKALI:
3. idan kuma zamui kallo na tsanaki da Hankali da Allah ya bamu zamuga cewa:
A. ta yaya wanda ya zamo shine shiriyar halitta baki daya ya gaza tsrear da Iyayen da suka tsuguna suka haifeshi?
B. shin in Allah swt zai baiwa Annabi saw dammar ceton dubban miliyoyin Alummarsa bazai yiwu ya sanya iyayensa ba?
C. a wajen dukkan musulmi na gari koda wannan Magana bata ci karo da Alkurani bam eye ribarsa na fadanta da yayata ta? Kana in Baban wani shugaba na Addini ne ko na sarauta ko na Mulki zaa rika wannan yayata Magana?.  
A karshe muna kira ga masu wannan mummunar Magana dasu fadaka iyayen Annabi saw ba wasa bane, kuma taba martabarsu na nuna cewa lallai akwai wata tsakaninka da Annabi saw.
Dole ka sanya Iyayen Annabi saw  cikinmatsayi uku:
1. su ahlin fatara ne baa aiko musu Manzo ba balle ace sunki binsa.
2. ko an rayasu sunyi imani dashi kamar yadda wasu riwayoyi suka nunar.
3. ko kuma sadda sukai wafati suna kan Addini HANEEFE na annabi Ibrahim as
وهما ناجيان من دون شك** فترة أو حياة أو حنفاء
ALHAMDULILLHI
والصلاة والسلام على رسول الله وآله وصحبه حق قدره ومقداره العظيم.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY