Yan Arewa na yiwa Junansu Bakin ciki
An cire Kano da Plateau daga masu amfana da Shirin gina yankunan da rikicin Boko Haram ya lalata.
Yan Majalisar wakilai na tarayya bisa takurawar yan majalisun Borno da makwabtanta sunyi kutu kutu wajen cire sunan Jihar Kano da Plateau daga wadanda zasu amfana da shirin gwamnatin tarayya na farfado da Yankin Gabas maso arewa da Rikicin Boko Haram ya lalata.
Wannan abin takaici anjiyoshi a bakin Sanata mai wakiltar Borno. Ali Ndume, wanda yana cikin masu wannan kudiri.
Tun kwanan baya dama yan yankin Gaba maso arewa sun nuna adawarsu karara akan raba Kano da Plateau cikin wadanda zaa tallafawa duk da cewa kuwa Kudirin kairkirar hukumar ma Sanatan Kano Rabiu Kwankwaso ne ya kawo shi.
Abin takaicin shine wadannan masu bita da kulli ga Jihar Kano sun manta gudunmawar da Kano ta bayar wajen tallafawa yan gudun Hijra,kai uwa da uba ma dai yadda Kanawa suka rasa dubbanrayuka da dukiyoyi sabili da wannan Rikici na Boko Haram.
Wannan na nuna crwa har yanzu jiki bai zamo magayi ba, kuma na nuna tsantsar butulci na wadancan jami'ai Jihohi da sukewa Jihar Kano da kuma bakin ciki karara.
Don haka muma muna kira ga Yan majalisun mu da Gwamnonin mu su san ta yadda zasu toshewa duk wani mai yi mana bita da kulli ko waye shi.
Duk wanda yai mana kan Kara wallahi sai mun masa na Itace.... Shege ka fasa.
Comments
Post a Comment