WAFATIN ANNABI SAW (15)

DABBOBIN MANZO (SAW) NA HAWA:

Akwai sabani cikin yawan dabbobin, akwai doki guda 10, akwai:- SAKABU, wanda akansa Manzo (SAW) yaje yakin Uhudu, MURTAJIZU, LIZAZU, wanda Mukaukis ya bashi da LAHIIFU DARABU, WARDU, MIRWAHU, SUBHATU, BAHRU, da sauransu.
Akwai kuma Alfadari wadda a cikin su akwai wata da Mukaukisu ya bashi ana kiranta:- DULDUL, ta rayu bayan wafatin Manzo (SAW) lokaci mai tsawo har ta tsufa hakoranta suka zube, Sahabban Manzo (SAW) sun zamo suna zuba mata garin sha'ir tana lasa, suna bakuntakarta a gidajensu don girmamawa gareshi (SAW) akwai kuma wata (FIDDATU) da S. Abubakar ya bashi.
Jaki kuma Manzo (SAW) yana da Afir da kuma Ya'afur.
TAKUBBANSA (SAW):
Yana da takuba tara 9 ga sunayen wasu daga ciki akwai Ma'asur shine farkon takobinsa sai ZUL KAFFAR mai baki biyu, da ALBATTAR wato mai yankewa da HATFU wato mutuwa akwai MUKHZAM da KADHID  da RUSUUB da ADB da KAL'AA.
MASUN SA (SAW):
Masun Manzo (SAW) hudu ne akwai mashi mai suna ALMASWA, saboda yana samun wanda aka soka daha da mutasanna da kuma wasu guda biyu.
SULKENSA (SAW):
Sulkensa bakwai ne akwai Zatul Fuduuli wadda ya daura ranar Badar da Hunainu, akwai Zatul Wishaahi, Zatul Hawashiy, Safdiyya da Fiddatu da Batra'u da Khiranku.
BAKANSA SAW:
Yana da Baka guda shida Zaura'u, Rauha'u, Safra'u, Shauhad, Katuum da Sada'ad.
SANDARSA SAW:
Yana da wata sanda da kanta yake a lankwashe, yana daukar abubuwa da kan sandar ana kiranta (Mihjanu).
TUFAFINSA SAW:
Manzo yayi wafati yabar tufafi biyu na hibra, da wani yadi na Yamen da litafi biyu (Suhariy) da riga itama Suhariyya, da wata (Suhuliyya) da Jubba 'yar Yamen da mayafi fari da huluna kanana uku ko hudu.
Manzo (SAW) yana da wata jaka da a cikinta akwai Madubinsa da Matajin kai da abin sakace da Asuwaki.
Yana da wata shimfida ta fata, anyi mata ciko da kaba yana da kofi mai fentin azurfa da wani mai fentin tagulla da wani na tangaran, sai daron wanka na tasa, da kwanon awo da yake auna Zakkar fidda kai dashi, da mudubi.
Manzo (SAW) yana da gado kafafunsa masu kyalli da kuma zoben azurfa da akayi masa shi a matsayin (Stamp) wato Khatim da yake buga wa akan wasikunsa akan zoben an rubuta.
محمد رسول الله.
(Allahu) a sama (Rasulu) a tsakiya sai (Muhammad) a kasansa, da sauran kayayyakin da Manzo (SAW) ya bari malamai duk sunyi bayaninsu dalla-dalla a manyan littatafai.   

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY