Manahilur Rashad tareda Shehu Atiku Sanka
Amsar Tambaya ta 17
tabbatar Watan Azumi yana zamowa ne ta hanyar radio ko Tarho ko kuma waya, daga nan sai ya game kowace nahiya kuma azumi ya lazimcewa duk wanda ya wannan tabbaci ya ishe shi, in ko yaketa ya ki yin azumito ranko da kaffara sun hau kansa, izuwa haka ne aksarin Malamai suka tafi na daga Fakihai. Masanin Allah sheikh Abdulmalik bin Usman as-singaly RA yana fadi a wata mazumarsa da ya bada fatawa da ita:
"1.azumi yana tabbata ta hanyar rura wuta kamar yadda ibnis Siraj ya fada ya kai aboki, 2. In har ala'ada (a gari) ta gudana da rura wuta lokacin da aka ga wata don haka batare da kokonto ba, 3. Haka yan tabbta ta hanyar Buga Bindiga a wajen Malama Rahuni ba tare da musu ba. 4. Haka ta hanyar wayar tangaraho a wajen Malam Illishu Babban Malami mai fatwa na Misra maabocin bincike, 5. Shine wanda ma ya wajaba kaffara ga duk wanda yai Musun wannan yaki yin Azumi,6. Mahdiyyu kuwa yace akwai duba cikin maganar Illishu amma lazimcewa Azumin duk sun hadu kansa, 7.abinda Illishu ya fada zancene ingatacce da ya yanke zancen duk mai zance...
Har inda yace"1 kace gamewar azumi ya gudane ne da zababbu a dukkan garuruwa, 2-3 Abdulbaqi ya fada cewaka duba zancen Manyan malamai na cewa koda mutum yai nisan mai nisan da yakai tafiyar zamani to baza ai izna da haka ba ba kuma zaai kokonton ittifaqi ba, 4, ka duba maganar sayyidi Dardiriy gwarzon Fakihai cikin bincike 5. Hakan shine sharren zance Allah ka datar damu kan daidai."
Hakika sheikh Muhammadu Bakhit al muti'i ya warware maganar a littafinsa "Irshad ahlilil millti ila isbatil Ahillati" hakanan Alkalin Alkalai na Dimashqa assayyid Abdul kafiy Assubkiy a littafinsa. "Al Ilmul manshur fi Isbatish Shuhur" kowanne ya tsawaita magana kan haka basu bar wani ba. Wadannan Littafai biyu duk an Buga su a Masar.
Intaha.
Comments
Post a Comment