Manahilur Rashad tare da Maulana Sheikh Atiqu Sanka



.
Amsar Tambaya ta 13



Muridin Tijjaniya yana da yanci cikin ziyarar wanda yaso daga Muqaddamai da neman Madadinsu da kuma Tabarrukinsu, da muzakarar Ilmai dasu matukar bai aikata wani abu daga abubuwa dake yanke Mureedi daga Darika ba! Domin su Muqaddamai masu izini ingatacce wakilai ne na Shehu Tijani RTA don haka neman Madadi dasu da Albarkarsu da Ziyartarsu duk neman Madadi ne da Shehu Tijani.
Muqaddamin dake Hana Mureedinsa Ziyarar waninsa daga Muqaddaman Darika to mai kuskure ne, kuma yana aikata abinda ke nuna rashin cikawarsa ga sharudan Taqdimi. Fadinsa na cewa wannan yana yiwa Muridi Salbun Darikarsa. Kuskure ne da Jahilci! Don kuwa ba wani daya dazai yanke Muridi daga Darika saidai Shehu Tijani RTA ko Annabi SAW. Ko in Muridi ya aikata daya daga sanannun sababan da suke yanke muridi.
Masanin Allah Babba Shahararren waliyyi sayyidi ALhaji Al-AHsan bn Muhammad As-susiy Al-Baaqiliy yana fada a cikin littafinsa. إراءة عراءس شموس فلك الحقائق العرفانية...
Bayan ya yi wani bayani kan Muqaddamai "sannan ba wani mutum dake da iko wurin cire wani daga sahabban shugabanmu daga Darika kkoda kuwa mai Laqqanawa ne,har sai dai in Manzon Allah SAW ne ya tsige shi sai Shehu Tijani ya cire shi sai kuma Khalifa ya cire shi a Fili da abinda yake ba wanin haka ba kuma fararwadomin ba Darika gareshi sai Dada sababin abinda aka Umar ce shi dashi kawai.
Masanin Alaah Sm Ahmad Sukairajuya fada A littafinsa
اليواقيت الأحمدية العرفانية
Amma muqaddami Idan ya daukewa wani Muridi Izini saboda wani dalili Na kashin kai na daga abinda bashi da Haqqi akan Muridin acikinsa to igiyarsa da shehu Tijani Bata yankewa don wannan daukewar izini indai Muridin ya tabbata akan sharudan Darika. Domi kasancewar Muaqaddami yana Laqqana wirdi ne wanda dashi ake samun Rabidah tsakanin Muridi Da Shehu Tijani RA, Muqaddami bashi da hannu bayan izini cikin yanke wannan Silar ta Muridi sai dai in an samu wani abu daga Muridi na daga abubuwa masu kore Darika da Alkawuranta.
Intaha.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY