SHI’A A MA’AUNIN ILIMI (3 / 1)

((Tattaunawa ta ilimi akan mas’alolin sabani tsakanin Sunnah da Shi’a))

SOYAYYAR AHLUL BAITI A CIKIN ALKUR’ANI DA HADISI

Soyayyar Ahlul Baiti, wadanda muke cewa da su “Sharifai” a Hausance yanki ne mai girma a cikin addinin Musulunci, Allah Mai girma ya umurci Sayyiduna RasululLahi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) da ya sanar da talikai haka, kana kuma shi ma kansa (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya bayyana haka a Hadisai masu yawa.. a game da bayyana daraja gami da girman su ne Allah Madaukakin Sarki yake cewa:

((ذلك الذي يبشر الله عباده الذين آمنوا وعملوا الصالحات قل لا اسئلكم عليه أجرا إلا المودة في القربى ومن يقترف حسنة نزد له فيها حسنا إن الله غفور شكور)) (الشورى: 23)

Ma’ana: ((Da irin wannan babban falala ce Allah yake yi wa bayinsa muminai masu biyayya da suka aikata ayyuka na gari albishir, ya Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ka ce: Ba fa na tambayar ku ba ni wani abu sakamakon wannan isar da sako nake yi maku, face soyayyar ku ga makusanta na, duk wanda ya aikata wani aiki mai kyau za mu rubanya masa da lada mai kyau, lallai Allah mai yawan gafarta zunubai ne, mai kuma yawan yabawa masu biyayya ne)) [as-Shurã’: 23].

An ruwaito Hadisi daga Abdullah bn Abbas (Allah ya kara yarda da su) yana cewa: lokacin da wannan aya: قل لا أسئلكم عليه أجرا إلا المودة في القربىى  ta sauka, sai suka ce ya Manzon Allah, su wane ne Allah ya umurce mu da sonsu? Ya ce: ((Fadimah da ‘ya’yanta biyu -Allah ya kara yarda da su-)). Duk da cewa wannan Hadisi yana da rauni, sai dai jamhur din malamai sun bayyana cewa Ahlul Baiti ake nufi a cikin wannan aya, ma’ana Sayyida Fadimah da ‘ya’yanta (Allah ya kara yarda da su), ta kuma hada da duk wadanda dangi ya hada su da su (Allah ya kara yarda da su baki daya). [Ibrãhim Sãleh al-Husainiy, Makãnatu Ahlil Baiti Alaihimus-Salãm wa Fadhlus Sahãbah RidhwãnulLãhi alaihim, Shafi: 7].

Haka ma Imam at-Tabariy ya kawo a cikin “al-Ausat” daga Abu Sa’id al-Khudariy (Allah ya kara yarda da shi) cewa, na ji Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) yana cewa: ((Ahalin gidana a cikinku tamkar jirgin Annabi Nuhu ne, wanda ya hau ya tsira, wanda kuma bai hau ba ya nitse)). Ya kuma cewa: ((Ahalin gidana a cikinku tamkar kofar Hidda ce ta Bani Isrã’ila, duk wanda ya shiga an gafarta masa)). [at-Tabaniy, al-Ausat: 6/406 – 5866].

Ad-Dailamiy ya kawo Hadisi daga Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya ce: ((Ku karantar da ‘ya’yanku dabi’u uku: soyayyar Annabinku, da soyayyar Ahalin gidansa, da kuma karatun Alkur’ani; domin lallai makaranta Alkur’ani za su kasance a cikin inuwar Allah, a ranar da babu wata inuwa sai tasa, suna tare da Annabawansa da Zababbun bayinsa)). [Kanzul- Ummal: 16/456 -45409].

Akwai ayoyi da Hadisai masu yawa ta suke tabbatar mana da wadannan ma’anoni da suke nuna muhimmancin wannan zababbiyar zuriya, zuriyar da Allah ya tsarkake su ya kuma tafiyar da duk wata kazanta ga barinsu..

Wannan ne ya sanya muka ga Sahabban Sayyiduna RasululLahi (Allah ya kara yarda da su) suna rige- irge wajen girmama mutanen wannan gida, suna kuma gabatar da su akan kansu, suna kwadayin sada zumunci na aure da su, domin samun girma da darajar da suke da ita..

Kafin nan, zai yi kyau mu kawo su wane ne ma Ahlul baiti, sannan daga baya mu fadi misalai na irin yanda Sahabbai suke rige- rige wajen yardar da su, da yi masu hidima.. Sannan mu bayyana bayani irin soyayyar da ya kamata mu yi masu.. kana kuma mu bayyana cewa soyayyar su ba tana nufin kin Sahabbai ba ne, kaman yanda son Sahabbai shi ma yana nufin kin Ahlul Baiti ba ne…

SU WANE NE AHLUL BAITI?

Wannan kalma ta “Ahlul Baiti” a Hausance ita ce “Iyalan gida”, kuma a duka harsunan biyun, (Larabci da Hausa) suna dauke ne da ma’anar: matar mutum, da kuma ‘ya’yansa.. Sai dai duk da haka idan aka danganta “Ahlul Baiti” da Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) a Shari’ance ana nufi: matansa, da ‘ya’yansa ne da sirikansa, da ‘yan uwansa (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam), saboda haka ne malamai suke cewa “Ahalin gidan Annabi” bayan matansa, su ne wadanda suka fitowa daga gidaje hudu: Ahalin Sayyiduna Aliyu, da Ahalin Sayyiduna Akilu, da Ahalin Sayyiduna Ja’afar, da Ahalin Sayyiduna Abbas (Allah ya kara yarda da su), da zaran aka ce “Ahlul Baiti”, to babu wadanda ake nufi in ba wadannan ba, in kuma waninsu ake nufi, to dole ne a fayyace.. [Ihsãn Ilãhiy Zahír, as-Shi’ah wa Ahlul Bait, Shafi: 36].

An ruwaito cewa Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya shigar da Sayyidatuna Fadimat da Sayyiduna al-Hasan da Sayyiduna al-Husain da Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da su) a cikin bargo lokacin da aya ta 33 cikin suratul Ahzab ta sauka, sannan ya ce: ((Ya Ubangiji wadannan su ne Ahalin gidana….)) [……]

Haka an ruwaito cewa Sayyiduna RasululLahi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya shiga dakin Sayyidatuna A’ishat (Allah ya kara yarda da ita) sai ya ce: ((Amincin Allah da rahamarsa su tabbata a gare ku ya Ahlal Baiti..)) sai ta amsa masa da: Amincin Allah da rahamarsa da albarkarsa sun tabbata a gare ka… [al-Bukhari, kitabut Tafsir].

AHLUL BAITI A WURIN SHI’A

Amma duk da wadannan ma’anoni na harshe, da ma Shari’a da wannan kalma take dauke da su, sai dai mazhabar Shi’ah “musamman Isna Ashriyya Imamiyya al-Musawiyya” sun takure ma’anar “Ahlul Baiti” ne da gida daya cikin wadannan gidaje hudun da muka ambata (wato gidajen: Aliyu da Akilu da Ja’afaru da Abbas), inda suka takaita ma’anar da gidan Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da su), shi ma a cikin gidan suka kara takaita ma’anar da ‘ya’yansa na wajen Sayyidatuna Fadimat (Allah ya kara yarda da su), bal ma kusan idan aka lura da kyau za a ga sun sake tsuke ma’anar wannan kalma, inda suka takaita ta da ‘ya’yan Sayyiduna al-Husain (Allah ya kara yarda da shi) shi kadai… kuma abu ne sananne cewa Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da shi) yana da wasu ‘ya’yan banda Sayyiduna al-Hasan da Sayyiduna al-Husain (Allah ya kara yarda da su), akwai: Sayyidatuna Zainab al-Kubrah, da Sayyidatuna Ummu Kulsum al-Kubrah (Allah ya kara yarda da su), dukansu -su biyun- ‘ya’ya ne na Sayyidatuna Fadimah ‘Yar Sayyiduna RasululLahi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ne, akwai kuma: Shugabanninmu, Muhammad (da ake masa lakabi da Bn al-Hanafiyya) da Abubakar, da Umar, da Usman, da Abbas, da Ja’afar, da Abdullahi, da Ubaidullah, da Yahya, dukansu ‘ya’ya ne na Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da su).

Ahalin gidan Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da shi) sun cigaba da wanzuwa a bayansa ta hanyar ‘ya’yansa guda biyar, wadanda su ce: Shugabanninmu, al-Hasan da al-Husain, da Muhammad (Bn Hanafiyya), da Abbas, da Umar (Allah ya kara yarda da su baki daya)..

Zai yi wahala ka iya samun wani dalili kwakkwara daga manyan malamai da litattafan Shi’ah akan wannan nuna bambanci da suka yi wajen zabo su wane ne Ahlul Baiti?!.. ka ga dai bayan fitar da gidaje uku cikin hudu da suka yi, a cikin gidan Sayyiduna Aliyu (Allah ya kara yarda da shi) ma sai da suka fitar da ‘ya’yansa mata na wajen Sayyidatuna Fadimah (Allah ya kara yarda da ita) kanta, balle kuma sauran ‘ya’yansa na wajen sauran matan da ya aura (Allah ya kara yarda da shi)!!

Sannan kuma, idan suka ce ana zamowa Ahlul Baiti ne ta hanyar haduwar mutum da jinin Sayyyiduna RasululLahi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam), to mene ne ya hana Sayyiduna Usman Zun- Nuraini (Allah ya kara yarda da shi) ya zamo cikin Ahlul Baiti, ganin cewa shi ma ya auri ‘Ya’yan Sayyiduna RasululLahi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) har biyu?!...

In kuma sun ce ana samun wannan falala ne ta hanyar ‘yan uwan uba, to mene ne dalilin fitar da Sayyiduna Akilu, da Sayyiduna Ja’afar, da Sayyiduna Abbas (Allah ya kara yarda da su)?!..

In ma sun ce ‘Ya’yan Sayyidatuna Fadimah (Allah ya kara yarda da ita) ake nufi, to ina suka baro Sayyidatuna Zainabul Kubrah da Sayyidatuna Ummu Kulsum al-Kubrah (Allah ya kara yarda da su)?!!!..

Duka wadannan tambayoyi ne da su ne suke farlanta kansu, suna kuma neman amsa daga masu riya wannan Magana ta Shi’ah..

Saleh Kaura
23/11/2016

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY