Wikileaks: Saudiya da Qatar ne suke daukar nauyin ISIS : wasikun Hilary Clinton

Ga mai son ganin emails din danna wannan

Shugaban Kamfanin nan mai kwarmata bayanan Sirri wato Wikileaks Julian Osang cewa wasu wasiku Yar takarar shugabancin Amurka Hilary Clinton sun bankado cewa Jami'an Gwamnatin Washington suna sane da cewa Kasar Saudi Arabia da Qatar sune suje daukar nauyin Kungiyar taadanci ta ISIS.

A wata hira ta Musamman da yayi da gidan talabijin na Rasha mai suna Russia today RT Julian ya bayyana cewa mun samu wasikun da Clinton ta rubutawa daraktan yakin neman zabenta John Bodista a farkon shekarar 2014 bayan saukarta daga mukamin ministan harkokin wajen Amurkan wanda a cikin wasikun take cewa dukkan gwamnatocin na Saudiya da Qatarsuna bada taimakon kudi ga DAESH. Yana mai cewa wannan bankada ta zamo mafi girna saboda irin Dalolin gwamnatocin biyu da suka shig cikin Duniya baki daya da kuma kafafen yada labarai
Shugaban na wikileaks ya cigaba da cewa "tabbas masana da masu sharhi a cikin gwamnatin ta Amurka suna sane da cewa wasu daidaikun mutane daga gwamnatocin saudi da Qatr sun taimaka wajen assasa kungiyar ISIS. Sai dai matsayin gwamnatocin biyu a hukumance ya rinka yin wala-wala da zilliya da cewa ai wasu Yayan sarakuna neda suka fandare ke amfani dukiyar man fetur na kasashen wajen taimakawa masu tsaurin raayi amma gwamnati tana Allah wadai da hakan.
Amma abinda muka gani a wannan wasiku- a ta bakin shugaban wikileaks- shine lallai hukomomin biyu sune suke daukar nauyin ISIS din kai tsaye.

Ya kara da cewa mutanen da suke bada gudunmawa ga gidauniyar Clinton sune dai mutanen da suke bada kudi ga DAESH.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY