WAFATIN ANNABI SAW 13



ANNABI (SAW) YANA RAYE DA RAYUWA TA MUSAMMAN:

Akwai hadisai fili da suke nuna cewa Annabi (SAW) yana raye, baya ga Alkur'ani da ya tabbatar da rayuwar Shahadai bayan kashesu Allah yana cewa:
                              آل عمران: ١٦٩
"kada kayi zaton wadanda aka kashesu cikin tafarkin Allah cewa matattune, bari su rayuyyu ne ana azurtasu a wurin ubangijinsu".
Akwai hadisai dake nuna duk sa'adda wani mutum yayiwa Annabi (SAW), salati to sai Annabi ya amsa masa.
Kazalika an rawaito cewa ana kawowa Annabi ayyukanmu ya gani, ya yaba da na gari ya nemi mana gafarar mummana, ga abinda Sheikh Yusuf Annabahani ke cewa a hamziyyarsa

ثم مات النبى بل أقلت شم
 
س الهدى واستمرت الظلماء.
  
جميع الأنام إلى الحشر
 
بليل نجومه الأولياء.
  
خيروه فاختار أعلى رفيق
 
لو أراد البقاء كان القاء.
  
وهو باق في الله في كل حال
 
قبل موت وبعد موت سواء.
  
لقى الله دون سبق فراق
 
إنما أكد اللقاء لقاء.
  
موته نقله لا على فأعلى
 
كل علياء فوقها علياء.
  
هو حرفى قبوه ولهذا
 
حرمت من تراثه الزهراء.
  
خصه الله بالحيات أكمل
 
حال يسير حيث يشاء.
  
كم رآه بيقظة ومنام
 
من محبيه سادة أصفياء.
  
ليس تبدو لعين شمس بماء
 
أو هو آء إلا وثم صفاء.
  
هو حى في قبره بحياة
 
كل حى منها له استملاء.
  

Saboda haka kuskure wani yace ai Annabi ya mutum irin mutuwar gama garin mutane, Allah yana cewa:
"                                                           النساء: ٦٤                                         
"Da dai su sa'adda suka zalunci kansu (alayin zunubi), zasu zo maka su nemi gafarar Allah Manzon (SAW) ya nema musu gafara, wallahi zau samu Allah mai karbar tubansu ne kuma mai jin kansu ne".
Wannan aya tana nan tana aiki ba sai a halin rayuwar Manzon (SAW) ba, kuma bayan wafatin Manzon (SAW), akwai wadanda suka zo suka nemi gafarar Allah a gaban kabarinsa kuma suka sami waraka.
An karbo daga Anas bin Malik (RTA) yace Annabi (SAW) yace:- "Rayuwata alherice a gareku mutuwata ma alheri ce a gare". (har sau uku), sai duk kowa yai shiru, can sai S. Umar bin Khattab yace "yaya haka zata kasance ya Rasullahi? Sai Manzon (SAW) yace rayuwata alheri ce a gareku; ana saukar min da wahayi daga sama sai in baku labarin abin da aka halatta muku da abin da ya haramta gareku, mutuwata alheri ce a gareku, ana bijiro min da aikinku duk ranar alhamis idan na alheri ne na gode Allah yasa haka idan na zunubi ne sai in nema muku gafarar zunuban ku.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY