WAFATIN ANNABI SAW (14)
GIDAN
ANNABTA:
Abin
da nake so bayani anan shine iyalan Manzon (SAW). ya auri S. Khadija bint Khuwailid,
wadda ta haifa
masa 'ya'yansa 6 wato Zainab, Rukayya, Ummu Kulsum, Fadima, Alkasim da
Abdullahi ta rasu kafin hijira da shekara uku.
Sannan
ya auri S. Saudat bint zainab bayan wafatin S. Khadija
da kimanin wata daya tayi wafati a shekara ta 54 bayan hijira.
Sai S.
Aisha bint Abibakar Assidik ya aurereta bayan Saudatu da shekara, tana 'yar shekara
bakwai ko shida, ya tare da ita tana da shekara tara, Manzon (SAW) bai auri budurwa
ba sai ita, ta zamo mafi ilimin matan Manzon (SAW), kuma tana daga wanda sukafi
kowa rawaitar hadisi daga Manzon (SAW) ta rasu hijira ta 57 ko 58 ranar 17 ga Ramadan
aka binneta a makabartar Baki'a.
Sai
S. Hafsat bint Umar binil Khaddab ya aureta a sha'aba shekara ta uku, ta rasu a
sha'aban hijira ta 45 tana da shekara 60 aka binneta a Baki'a.
Sai Zainab
bint Khuzaimah AL HILALIYYAH (UMMUL MASAKIN) ya aureta shekara ta 4 ta rasu bayan
wata uku da auren aka binneta a Baki'a.
Sai
Ummu Salma Hindu bint Abi Ummayya, itama ta shiga cikin matan Annabi a shekara
ta hudu, tana daga mafi ilimin matan Manzon (SAW), kuma itace mafi hankalinsu
ta rasu shekara ta 59 baya hijira, aka binneta a Baki'a shekarunta 84.
Sai
Zainab bnt Jahsin itace matar Zaid bin Harisata da ya saketa Allah ya aurawa
Annabi ita, ita kuma tafi kowa yawan ba a matan Manzon (SAW) ta rasu shekara ta
20 tana da shekara 53.
Sai Juwairiyyah
bintil Haris, an kawota a cikin ribatattun Banil Musdaluk sai ta fada cikin
rabon Sabit bin Kais bin Shammas, sai ya daura mata fansa, saboda haka ta taho
wurin Annabi (SAW) inda ta nemi taimakonsa, shi kuma ya nemata da cewa zai biya
fansarta ya aure ta nan take ta yarda ta rasu a Rabi'ul Auwal shekara ta 56
tana da shekaru 65.
Sai Ummu
Habiba Ramlat bint Abi Sufyan ta zamo matace ga Ubaidullahi bo Jahsh, sunyi
hijira zuwa Habasha, amma sai yayi ridda acan ya koma kirista ya mutu a haka,
sai Manzon (SAW) ya nemi aurenta, shekara ta 7 ta rasu a hijira ta 44.
Sai Safiyyatu
bint Huyayyu bn Alkdaba, ita kuma an kamata ne a cikin ribatattu lokacin yakin
Khaibara, mahaifinta shine shugaban Yahudawan Banun Nadeer, sai Manzon (SAW) ya
zabeta ya bijiro mata da musulunci ya karba ya aure ta, ta rasu rasu a hijira ta
50.
Sai
matarsa ta karshe wato Maimuna bintil Haris, Manzon (SAW) ya aureta a lokacin (Imratul
Kada'i) a Makka, ta rasu a wurin da ake kira (SARAF) kimanin Mil tara daga Makka shekara ta 51 kabarinta yana nan.
Wadannan
sune matan da Manzon (SAW) ya auresu, kuma ya tare da dasu, su 11 ne kuma yayi wafati
ya bar mata tara, biyu sunyi wafati a rayuwarsa.
Akwai
kuma sadakun Manzon (SAW) wanda a cikinsu akwai MariyatulKibdiyya, mahaifiyar Ibrahimul
Mu'azzam, sai kuma Raihanatu Bint Zaid Alkuraziyya.
'YA'YAN
MANZON (SAW):
'Ya'yan
Manzon (SAW) kamar yadda ya gabata su bakwai ne, maza uku mata hudu ga su kamar
haka:
Alkasim,
shine babba a maza, dashi ake yiwa Manzon Allah (SAW) Alkunya wato ace (Abul
Kasim), an haife shi kafin aiko Manzo (SAW) kuma ya rasu kafin aikoshi da shekara
2.
Abdullahi,
ana kiransa Tayyib ko Tahir shima ance kafin Annabta aka haifeshi, wasu kuma
sukace a'a bai riski musulunci ba.
Sai
Ibrahimal Mu'azzam wanda aka haifa
a Madina ya rasu yana da kwana 70.
Sai matan
akwai Zainab wadda Abil As binir Rabi'in ya aureta, sai Rukayya da Ummu Kulsum
da S. Usman ya aure su daya bayan daya duk suka rasu, sannan Fadima wadda take
matar S. Ali ce mahaifinyar Hasan da Husain, dukkan 'ya'yan Manzo (SAW) sun
rasu a rayuwarsa sai dai S. Fadima kamar yadda ya gabata tayi wafati bayan
Manzo (SAW) da wata shida.
Comments
Post a Comment