Manahilur Rashad tare da Shehu Atiku sanka Amsar Tambaya ta 16






Amsar wannan Tambayarnan kamar amsoshin da suka gabata ne, don na fada cewa gaba dayan Mukaddamai Na;ibai ne na Shehu RTA kuma mukai bayanin hanyar da ake cirata daga Muqaddami zuwa waninsa, tare da Ladabi garesu cikin hakan,to tunda suka zamo Na'ibai na Shehu to cirata daga wani bai zama yankewa ne da yake jawo aibi da lefi ga Muridi, sai dai fa in ya Munana Ladabi ga Na farko to anan sai ya zama mai Munanawa ga Shehu RTA wal iyazu billah,sawa-un Muqaddamin yana Raye ko kuma ya Mutu, Shehu Tijani RTA har tare da Muridansa yan jibintar Tarbiyarsu da kansa Allah ya yarda dashi ya kara mana Aalbarkarsa!
Sannan bai kamata ga Muqaddamai su Rika ganin Kansu, da fifikonsu akan Muridansu, ko baiwa akansu saboda sun karbi Darika a hannunsu, wannan yana nuna rashin cancantarsu da cika sharudan Muqaddamanci, Darika dai ta Shehu Tijani ce ba wani falala ga wani a cikinta kan wani, amma ana neman Ladabi daga Muridai a janibin Wakilan Shehu Tijani, tare da tsayawa da sharudanta da cika Alkawuranta,
Ba'aqiliy yana fada cikin hakkin Muqaddami da abinda ake nema daga gareshi cikin littafinsa Ira'atil Ara'is cewa yayin da ya zama yantacce daga bautar wani sai Ubangidansa ya kafa shi don zamowa mai Shiryarwa gareshi,yana mai kudure cewa shi bashi da wata Shiriya, yana mai Dogaro kan abinda yake boye cikin ilmin Maulana, ta yadda bai ganin wata falal gareshi kan wanda ya bishi don kansa. Yana mai yanke da cewa shi abin sauwakewa ne abin yaSsarewa ne don wannan aiki daga Shugabansa da qahariyya, kuma Allah ya rubuta abinda. Ya hukumta, wanda wani abu ya rigaya a ilmin Allah to samunsa da waninsa abin yankewa ne kuma umarni da kyakyawan aiki da Hani da Mummunan aiki wata Siyasa ce Ta Allah don Bayyana Ladabi daga Sarakuna da Wadanda ake Bawa Umarni kawai (da Allah yaso sai ya Sanya ku Al'umma daya) shine ainahin abinda muka fada, kuma hakan Budewa ne ga Basirar masu shiryarwa da wanda ake shiryarwa3, (ba wani abu a hannunka da Lamari) hukumci yankakke ne ga nauo'in baiwa akan halittar Allah da Risala da Shehunta da wa'zantarwa da Limanci da da Izinai, da duk kowane nau'in Matsati na addini da tsare tsare na Taklifi, ga dukw,da Allah ya dora masa rainon wani shi tun daga iyaye da shuwagabanni. Akan Wadanda suke Mallaka da kuma dabbobinsu, da duk abinda yake da Haqqi akan waninsa, (yin gori akan abin jibinta yana daga abubuwa masu Bata aiki,) haka nan akan Muridai da daliban Ilimi da koyarwa. Ya wajaba akan kowane Muridi yaga kansa a matsayin mai yin hidma ga shehinsa. Kawaikuma magani gareshikuma bashi da wata masalaha cikin sa, sai dai kawai abinda Aizo masa daga halarar Shehin nasa na Martabobi daga Allah kada ya Dada kada ya rage mai yiuwa Shedan ya zayyana masa cewa "ina da Yaya a gari kaza ko na laqqanawa wane a gari kaza ko Darika ta bayyana a hannuna Alhamdulillahi, don dama Maqasudinsa shine Riya da daukaka kansa akan waninsa, Don ita Darika itace mutum ya zage kansa daga NAFSU da duk abin sa ya lazimce mata"
Hakika Ba'aqiliy ya tsawaita magana anan Allah ya saka masa da Alheri bisa wannan Darika Ahmadiyya

Wassalam!

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY