WAFATIN ANNABI SAW KASHI NA KARSHE (17)
YAKOKIN
RIDDA/HURUUBUR RIDDATI:
Yaduwar
labarin wafatin Manzo (SAW) koda wuya a cikin Jazirar larabawa, sai da yawan
kabila sukayi ridda daga Musulunci suka koma kan addinansu na bautar gumaka,
musamman kabilun da basu dade da shiga Musulunci ba, inda wasu kuma aka sami
Annabawan karya a cikinsu, wasu ma kuma tun a karshen rayuwar Manzo (SAW) sukayi
da'awar Annabta kamar Musailamatul Kazzab da Aswadul Ansiy, inda wasu kuma suka
hana zakka.
Sababin
riddan nan zamu iya tsaresu ga cikin da dalilai masu zuwa kamar haka:
1- Da
yawa daga kabilun larabawannan sun shiga addinin Musulunci ne a karshen rayuwar
Manzo (SAW) bayan bude Makka, saboda haka akida da dabi'un Musulunci basu dasu a
cikin zuciyarsu ba.
2- Musulunci
yayi musu tsarin bin gwamnati guda wanda hakan basu saba dashi ba ba sunfi
sabawa da tsarin kabila – kabila.
3- Musulunci
ya wajabta musu fidda zakka wanda suke ganin hakan kamar wani haraji ne, sabida
haka dajin cewa Manzo (SAW) ya koma ga Allah sai suka hana duk wani hakki na zakka
da suke bayarwa zamanin Manzo (SAW), saboda haka S. Abubakar (RTA) ya shawarci Sahabbai
kan me zai aikata dasu, inda suka ki ya yakesu saboda suna yin sallah da wasu abubuwan
na Musulunci, shi kuma yaki inda yace, duk wanda ya raba tsakanin sallah da
zakka to yayi ridda, saboda duk inda Allah (SWT) yace ku tsaida sallah zaice ku
bada zakka. A karshe dai Sahabbai suka amince aka yaki irin wadanda suka hana
zakka.
4- Musulunci
ya hana musu wasu abubuwa da zuciyoyinsu suka dasu akansu, kamar zina, caca,
shan giya, da sauransu, saboda haka da jin labarin wafatin Manzo (SAW) suka koma
kan wadancan dabi'u.
5- Bayyanar
Annabawan karya, a tsakanin kabilun larabawa ya janyo mutane suna bin Annabin karya
da ya bayyana a kusa dasu daga cikin irin wadannan akwai Musailamatul Kazzab,
Aswadul Ansiy, Sajah Attamimiyya, Dulaiha bin Khuwalid Al asadiy, kazalika a
Yamen akwai Aihalutul Aswad.
Dukka wadannan kabilu da Annabawan karya s. Abubakar yaga
bayansu inda ya tara runduna mai yawan gaske, sannan ya kasasu gida goma sha daya
ya aika dasu zuwa ga masu ridda, daga cikin kwamandojin rundunonin nan akwai Khalif
binil Waleed, Ikramatu bin Abi Jahl, Shurahbilu bin Hasanah, Muhajir bin Abi Umayya,
Huzaifatu bin Muhsinin, Arjafatu bin Harsamata, Suwaidu bin Mikranin, Ala'u binil
Hadramiy, Khalid bin Sa'eed, Amru binil As Duraifatu bin Hajizin.
Wadannan sune kwamandojin rundunonin sha daya 11 can da
aka aika don yakin ahlin ridda, aka rubuta musu daftarin da zasu yi amfani
dashi (wato takardar yaki) iri daya kowa ya fita izuwa inda aka umarce shi ya
tafi inda kowa ya dawo cikin nasara, aka kashe Musailamatul karkashin Khalid binil
Waleed, haka nan aka kashe Aswad Al Ansiy wanda aka kashe karkashin Mujahiru bin
Abi Umayya, shi kuwa Dulaiha bayan da aka tarwatsa rundunarsa sai ya gudu zuwa Sham
(Syria), wato daukar FARISA tare da Musulmi, amma Sajah da mutanen ta banu
Tamim da aka tarwatsa su itama ta gudu inda daga baya akace ta tuba ta Musulunta.
Haka dai aka shafe kusan shekara guda ana yakin ridda, Allah
(SWT) ya bawa rundunonin Musulmi nasara.
To da haka dai S. Abubakar yayi saura sake hade kan jazirar
larabawa karkashin tutar La'ilaha illallahu Muhammadar Rasulullahi (SAW), bayan
da ta tasamma wargatsewa sakamakon labarin wafatin Manzo (SAW) inda S. Abubakar
ya nunawa duniya cewa Musulunci bai kare da wafatin Manzo (SAW), bari ma yanzu
ya fara watsuwa shi yasa ana kammala yakokin ridda sai aka fada bude daulolin duniya
inda S. Abubakar ya aikawa da rundunonin don isar da sakon Manzo (SAW) izuwa
inda bai jeba a rayuwar Manzo (SAW) da shigar dashi dukkan sako da lunguna da
nahiyoyin duniya.
KHATIMA/CIKAWA:
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da ya bani dama na
rubuta wannann 'yar makala data danganci Tarihin Wafatin Manzo (SAW) da abinda
ya biyo bayanta na maganar Khalifanci da kuma yakokin ridda (APOSTACY WARS),
duk abin da aka gani a wannan littafi ba zancena bane ko tsarina, abubuwa ne da
malamai na tarihi suka rubuta a littafansu na ciro nayi tarjamarsu zuwa hausa
na kuma jerasu gwargwadon ikona, abinda nayi dai-dai daga Allah ne, kuma shi
nake fatan ya sakamin, wanda nayi kuskure daga nine, saboda gajiyawa ina neman
gafarar Allah, kuma ina neman a nabbahar dani.
Allah kayi salati ga Shugaban Talikai Annabi Muhammadu
(SAW) da Ahlin gidansa da Sahabbansa masu yaki don dauka addininsa da sakonsa
ba dare ba rana, ka kara yarda da wanda ya biyo hanyarsa na daga Auliya'u kamar
Shehimmu Ahmad Tijjani Abul Abbas Ashshariful Hasniy da Khalifansa S. Ibrahim
Inyas, kajikan iyayenmu da suka raine mu tun muna ciki har girmanmu kasaka musu
da alheri ka taramu baki daya a gaban Annabi Muhammadu (SAW) ranar gobe kiyama.
Alhamdu Lillahi Rabbil Alamina, Wassalam.
Dan
uwanku:- MUHAMMAD DAHIR LAWAN MU'AZ ATTIJANEEY ZANGON BARE-BARI, KAO NO.196
08060306021. 12:27 na ranar JUMA'A 27 RAJAB, 1428 A.H. 10 AUGUST, 2007.
Comments
Post a Comment