SHI’A A MA’AUNIN ILIMI (1) Dr Saleh Kaura
((Tattaunawa ta ilimi akan mas’alolin sabani tsakanin Sunnah da Shi’a))
GABATARWA
Bismilãhir Rahmãnir Rahím
Godiya ta tabbata ga Ubangijin Tãlikai… Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Abin tinkahonmu, Annabi Muhammadu, wanda da shi ne Allah Madaukakin Sarki ya jiyar da kuramen kunnuwa, ya kuma bude rufaffun idanuwa, ya haskaka dodaddun zukata, suka ji, suka kuma ga shiriya, kana kuma suka rungumeta hannu bibbiyu.. Tsira da amincin su hada da almajiransa –Alaye da Sahabbai- da suka sami tarbiyya ta kai-tsaye daga gare shi, hakan ya ba su daman darewa wani babban matsayi da Allah ya fifita su da shi akan dukan talikai, wannan kuma ya samu ne bayan sun yi imani da shi, suka kuma mara masa baya, suka taimake shi, suka kuma bi hasken da ya zo da shi sau da kafa..
Godiya ta tabbata ga Ubangijin Tãlikai… Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Abin tinkahonmu, Annabi Muhammadu, wanda da shi ne Allah Madaukakin Sarki ya jiyar da kuramen kunnuwa, ya kuma bude rufaffun idanuwa, ya haskaka dodaddun zukata, suka ji, suka kuma ga shiriya, kana kuma suka rungumeta hannu bibbiyu.. Tsira da amincin su hada da almajiransa –Alaye da Sahabbai- da suka sami tarbiyya ta kai-tsaye daga gare shi, hakan ya ba su daman darewa wani babban matsayi da Allah ya fifita su da shi akan dukan talikai, wannan kuma ya samu ne bayan sun yi imani da shi, suka kuma mara masa baya, suka taimake shi, suka kuma bi hasken da ya zo da shi sau da kafa..
Bayan haka, wannan bayani ne da yake son ya tabo matsalolin da suke da ruwa da tsaki wajen kara fadada sabanin da yake tsakanin matafiyar “Ahlus-Sunnah wal jama’a” –wadanda su ne kashi 90 % na al’umman Musulmai a duniya- da matafiyar “Shi’a” –da suke su ne kashi 10 % na Musulmai baki daya-… Na sha alwashin wannan bayani ya zamo na ilimin da babu hauragiya, balle hauma-hauma; saboda haka, manufofin da wannan rubutun yake son ya cimma –bayan neman yardar Allah ta hanyar neman gaskiya- su ne kamar haka:
1. Kara kusanto da al’umman Musulmai da junansu, ta yanda za su aiwatar da kiran da Allah Madaukakin Sarki ya yi masu na hadin-kai a cikin Alkur’ani Mai girma, da kuma kiran da Sayyiduna RasululLãhi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya yi masu a cikin Hadisai..
2. Bayyana wa al’umman Musulmai –Ahlus-Sunnah- ainihin matsalolin da suke zamowa cikas wajen samun wannan hadin kai da aka ba su umurni, saboda su yi watsi da wadannan matsaloli.
3. Kira zuwa ga ‘yan uwanmu ‘yan Shi’a, kan su sake nazari akan wadannan matsaloli da suke hana zartar da ma’anar ayoyi da Hadisan hadin kai a aikace.. su dawo su kalle su irin kallon da Shugaban Ahlul- Baiti Sayyiduna Aliyu bn Abudalib (Allah ya kara yarda da shi) ya kalle su.
Matashiyar wannan bayani kuwa ita ce:
1- Yarda da Musuluncin duk wanda ya furta kalmar “Lã’ilãha illalLãhu Muhammadur RasululLãhi”, muddin ba ya fita daga Musulunci da ganin damansa ta hanyar ridda ba ne, ko ya yi inkarin abin da ya tabbata a cikin Musulunci ta hanyar tawaturi ba tare da tawili ba..
2- Ana kira zuwa ga Allah Madaukakin Sarki ne a karkashin inuwar soyayya ga kowa da kowa, gwargwadon irin kusancin sa ko dangantakar sa da Allah mai girma da daukaka, domin soyayya ce za ta sanya mai kira zuwa ga Allah ya kira waninsa ya zo ya yi imani, domin ya sami ni’imar kwanciyar hankali da natsuwa, da lada irin wanda ya yi imani da shi.. Sam babu kiyayya -ko kadan- a cikin hanyar kira zuwa ga Allah, in ma akwai wani abu da ya zamo dole mu ki shi, to lallai bai wuce ita kiyayyar kanta ba, kaman yanda Ustaz Badi’uz- Zaman an-Nurusy ya fada.
Wannan kenan, tun bayan rikicin da ya faru tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan Shi’a masu biyayya ga Malam Ibrahim Alzakzaki a karshen shekaran da ta gabata, da kuma rikicin da ya biyo bayan matakin da gwamnatin Kaduna ta dauka na haramta kungiyar Shi’a da take biyayya ga Malam Zakzaki ne, aka sami wasu suka fito fili suna zargin Malamai da Shaihunan Sufaye na kasar nan da cewa ba sa tsoratar da al’umma akan hatsarin mazhabar Shi’a da suke yada zagin Sahabbai, wannan zargin ba wai kawai daga wajen gidan Sufaye ne ya fito ba kawai, bal ma har da wasu almajirai daga cikin Sufayen… Mun kalubalanci wannan tunani da wasu bayanai na lacca da na rubutu da manyan malaman kasar nan suka yi, suna masu nuna hatsarin yaduwar zagin Sahabban Ma’aikin Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam), wadanda suka sami shaida daga gare shi, Alkur’ani mai girma ma ya dawwamar da ambatonsu.. sun yi haka tun nesa da kofa, ba kuma su daina yi ba, ba kuma za su daina ba.. Bambancin Malamai da Shaihunan mu da wasu shi ne, su suna kira ne cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, da kuma fatan Allah ya sa a gane a kuma amsa… a daidai lokacin da wasunsu so suke su muzanta, ko su ci mutunci wanda suke kira, abin da zai sanya a karshe ya dode kunnuwansa ga barin sautinsu.. Malaman mu da Shaihunan mu suna fada da cuta ne, ba da mara lafiya, suna kin sabon Allah ne ba kin mai sabo ba..
Haka ne, lallai gaskiya ne a cikin mutane akwai wadanda ba su samun natsuwa sai sun dagula ruwa ya cabe, sannan suke iya yin sú, saboda biyan bukatun kawunansu… Wasu kuma ba sa iya yin sú sai sun samo sinadarin alif sun jefa a cikin wannan dagulallen ruwa ya kwanta, sannan su tãce shi ya dawo kashar-kashar, ta yanda za su iya hangen duk abin da yake ciki, ba kuma tare da launi, ko dandano, da kamshinsa sun sauya ba, sannan su yi sú dinsu, masu tsarki su yi, masu wanka ma su yi, masu sha da wanki duk su yi…
Ina ga wannan bambancin ne ya sanya -a baya-, aka ji muryar masu dagula ruwa –game da mas’alar “Ahlus- Sunnah” da ‘yan Shi’a- ta dan hau sama, komai ya cabe, mutane da yawa suka gaza wajen rarrabe tsakanin gaskiya da karya, abin da ya sanya masu tãce ruwan da tsaftace shi jinkirtawa, suka dan saukar da muryoyinsu kasa kadan, har yanayi ya sauya, hayaniyar kuma ta kwaranye; domin su samu su cigaba da nasu aikin cikin tsanaki, suna masu amsa kiran Allah Madaukakin Sarki da yake cewa:
((قل هذه سبيلي أدعو إلى الله على بصيرة أنا ومن اتبعني فسبحان الله وما أنا من المشركين..)) (يوسف: 108)
Ma’ana: ((Ka ce wannan dai ita ce hanyata, ina kuma kira zuwa ga Allah –Ta’ãla- ne akan basira, ba ni daya ba, har da wadanda suka bi ni, lallai na tsarkake Allah daga dukan nakasu, sam ba ni a cikin masu hada Allah da wani a wajen bauta)) [Yusuf: 108].
Musulmai a duk inda suke akwai wasu mahada da suka hada su gaba dayansu, duk kuwa da bambancin ra’ayi da fahimta da suke a tsakaninsu, wadannan mahadai su kansu suna amsar sabani, ba kuma tare da an fita daga inuwar bishiyar Musulunci da ta lullube kowane Musulmi ba, mahadan sun hada da:
MAHADIN AKIDA: A tarihin Musulunci an sami mazhabobi mabambanta na Akida, wadanda suke bin hanyoyi mabambanta wajen isar da Akidar Musulunci ga al’umma.. hakan kuma ya bude wa hankulan Musulmai kofofi masu yawa na sanin ginshikan Akida, da kuma bayanai na dalla-dalla a bangaren ilimin Tauhidi da Usuluddini, ba kuma tare da wasu sun kafirta wasu, ko su kore su daga inuwar Musulunci ba.
MAHADIN SHARI’A: A bangaren shari’a ma tarihin Musulunci yana sane da mazhabobi mabambanta da suka yi aiki wajen fitar da hukunce-hukuncen ayyukan bayi na ibada da na mu’amala, inda suka yi aiki a cikin furu’a, ba kuma tare da sun bar tabbatattun abubuwan da addinin ya kafa su ba, abin da har ya kai malaman ko iyayen da mazhabobin suke komawa zuwa gare su suke fadin cewa “fahimtata daidai ce, amma za ta iya zama kuskure, fahimtar wanina kuskure ne, amma za ta iya zama daidai”.
MAHADIN AL’UMMA: A bangaren al’umma kuwa, dubi irin yanda muka bambanta a launi da harshe, dukanmu kuma Musulunci ya hada mu, ya kuma daidaita tsakaninmu a wajen daraja da matsayi, babu wanda ya dara wani sai sai idan ya fi shi tsoron Allah, ba kuma ma kyashin wani daga cikin mu ya shugabance mu, alal misali: ga Sayyiduna Bilal bn Rabah, bakar fata daga Habasha “Ethiopia”, ga Sayyiduna Salmanul Fãrisi daga Fãrisa “Iran da makwabtanta”, ga Sayyiduna Suhaibur Rúmí, Baturen Roma “Italy” (Allah ya kara yarda da su) dukansu a gaban Sayyiduna RasululLãhi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) kafada da kafada da Larabawa… Hakazalika, ga Salahuddin al-Ayyubi [532 – 589 H/ 1137 – 1193] Bakurde, shi ne ya hada kan Larabawa da sauran Musulmai, ya kuma shugabance su a yakin “Salibiyyin”.. ya kuma zamo gwarzo da al’umman Musulmai suke alfahari da shi…
MAHADIN HADHARA: A wannan fagen kuwa, kowa ya san irin yawan bambancin al’adu da wayewa da ake samu a tsakanin Musulmai, abin da har ya sanya Imam al-Shafi’i (Allah ya kara yarda da shi) ya sauya wasu daga cikin fatawowin da ya bayar a lokacin da yake Iraki, bayan ya dawo kasar Misra da zama, hakan ya sanya aka sami kashi biyu na mazhabar Shafi’iyya, akwai tsohuwar mazhaba –lokacin yana Iraki- da kuma sabuwar mazhaba, wato bayan ya dawo Misra har zuwa karshen rayuwarsa.. Amma duk da haka mahadar Musulunci ya daure su a karkashin bishiyar Musulunci, ba kuma tare da an kori kowa ba.
MAHADIN KASA: Duk inda Musulmi ya shiga a cikin kasar Allah inda ‘yan uwansa Musulmai suke rayuwa kasarsa ce, koda kuwa ya fito daga wancan yanki zuwa wannan ne.. ‘Yan mulkin mallaka ne suka tsiri wadannan katangogi suka tsattsaga kasarmu, suka mayar da su kasashe; saboda kawai su ji dadin lakume mu da yi mana dauki dai-dai…. [Muhammad Imãrah, Adhwã’un alã al-Maukifis Shiy’ey min As’hãbi RasululLãhi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam), shafi: 5-7]
To, ashe za mu iya rayuwa karkashin inuwa daya, cikin mutunta juna, duk kuwa da sabanin ra’ayi, da bambancin fahimta, kaman yanda iyayenmu da kakanninmu suka rayu a cikin irin wannan yanayi, ya kuma zamo masu ni’ima da jin dadi a tsawon tarihi mai nisa.
Saboda haka, kafirta Musulmi da nesanta shi ko korarsa daga karkashin inuwar Musulunci shi ne babban abokin gaban wannan ni’ima da Allah Madaukakin Sarki ya yi wa al’ummar Musulmai.
Manufarmu ta yin kira zuwa ga Allah ita ce isar da sakon Allah cikin hikima da kuma kyakkawan wa’azi da fadakarwa, idan ma za a sami sa-in-sa, to abin da zai haifar da da mai ido za a yi, ba manufarmu ne mu bakanta ran wanda muka saba da shi a fahimta ko ra’ayi ba, ba kuma manufarmu ne mu guma masa bakin ciki ba, manufar ita ce a ce hasken da ya same mu ya same shi, ya rabauta kaman yanda muka rabauta… ko kuma alal akalla, ya san cewa muna yin addininmu ne cikin basira da hujja, karkashin inuwar ijtihadi –wanda ya cika daukacin sharuddansa- ba wai son rai ba…
Manufarmu ta yin kira zuwa ga Allah ita ce isar da sakon Allah cikin hikima da kuma kyakkawan wa’azi da fadakarwa, idan ma za a sami sa-in-sa, to abin da zai haifar da da mai ido za a yi, ba manufarmu ne mu bakanta ran wanda muka saba da shi a fahimta ko ra’ayi ba, ba kuma manufarmu ne mu guma masa bakin ciki ba, manufar ita ce a ce hasken da ya same mu ya same shi, ya rabauta kaman yanda muka rabauta… ko kuma alal akalla, ya san cewa muna yin addininmu ne cikin basira da hujja, karkashin inuwar ijtihadi –wanda ya cika daukacin sharuddansa- ba wai son rai ba…
Duk da haka, ba za mu nesanci gaskiya ba -ko kadan- ba kuma za mu butulce mata domin kawai mu dadada ran wani ba, za dai mu bi hanyar da hankali da kuma fidira za su aminta da su wajen tattaunawa cikin tsanaki, karkashin inuwa ta mutunta juna.. Kaman dai yanda muka gada daga shugaban masu kira zuwa ga Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam).
Saboda haka, bayanan za su zamo a tsare kaman haka:
Gabatarwa.....
Mene ne Shi’a, kuma su wane ne ‘yan Shi’a? da rarrabe-rarrabensu.
Shi’a a matsayin mazhaba ta furu’a.
Shi’a a matsayin mazhabar Akida
Muhimman matsalolin da suke kawo cikas wajen hadin kai tsakanin Ahlus- Sunnah da Shi’a tare da bayanin hukuncin da ya rataya da su a Shari’ar Musulunci, wannan maudhu’i zai tabo:
1. Sabani a mas’alar Shugabanci “Imamah” ko “Halifanci”.
2. Sabani akan Alkur’ani Mai girma.
3. Sabani akan Hadisan Manzon Allah masu daraja.
4. Sabani akan ma’anar “Takiyya”
5. Sabani akan Fikhu “furu’a”
6. Sabani akan Sahabban Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam).
Hukuncin kafirta Musulmi a Shari’ar Musulunci.
Dangantakar da Allah ya shimfida tsakanin Musulmai..
1- Nasiha ta gaskiya, da nasiha da hakuri a tsakaninmu
2- Yi wa wadanda suka gabace mu a fagen imani addu’a.
3- Kiyaye addini da kyau domin sanar da masu zuwa a bayanmu.
Muhimmancin hadin kai tsakanin Musulmai baki daya, koda kuwa suna da sabanin ra’ayi.
Mene ne Shi’a, kuma su wane ne ‘yan Shi’a? da rarrabe-rarrabensu.
Shi’a a matsayin mazhaba ta furu’a.
Shi’a a matsayin mazhabar Akida
Muhimman matsalolin da suke kawo cikas wajen hadin kai tsakanin Ahlus- Sunnah da Shi’a tare da bayanin hukuncin da ya rataya da su a Shari’ar Musulunci, wannan maudhu’i zai tabo:
1. Sabani a mas’alar Shugabanci “Imamah” ko “Halifanci”.
2. Sabani akan Alkur’ani Mai girma.
3. Sabani akan Hadisan Manzon Allah masu daraja.
4. Sabani akan ma’anar “Takiyya”
5. Sabani akan Fikhu “furu’a”
6. Sabani akan Sahabban Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam).
Hukuncin kafirta Musulmi a Shari’ar Musulunci.
Dangantakar da Allah ya shimfida tsakanin Musulmai..
1- Nasiha ta gaskiya, da nasiha da hakuri a tsakaninmu
2- Yi wa wadanda suka gabace mu a fagen imani addu’a.
3- Kiyaye addini da kyau domin sanar da masu zuwa a bayanmu.
Muhimmancin hadin kai tsakanin Musulmai baki daya, koda kuwa suna da sabanin ra’ayi.
Saboda haka, zai yiwu a fadada wannan rubutun, zai kuma yiwu a tsakaita shi, gwargwadon bukatar haka, ko rashin bukatar haka.
Ina rokon Allah Madaukaki ya ba ni ikon gabatar da wannan muhimmin bayani a karkashin tsantsar ilimi da hujja, ya nesanta ni da son rai, ko neman bakanta wa wani, ya kuma tsarkake mini niyyata ta zamo ta fuskance shi –shi kadai- cikin tsarki da tsafta, ya kuma hada kan al’umman Sayyiduna RasululLãhi (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) baki daya, amin.
Saleh Kaura
7/11/2016
7/11/2016
Comments
Post a Comment