Manahilur Rashad tare da Maulana Sheikh Atiku sanka
Amsar Tambaya ta sha Hudu 14
Wannan amsa itace ainahin Amsar tambaya da ta gabata, saidai anan akwai Karin bayani wanda shine ya wajaba ga Muqaddami in yaga wani wanda ya fishi daukaka a Darika da yawan sani to ya ciratu zuwa gareshi tare da Muridansa, kammar yadda yake an ambata a cikin littafan Darika. Fasali guda kan haka Yazo a littafin Rimahu na sayydi Umar Al Futy- sannan in yaki yin haka don Girman kai ko wani abu na daga lamura na NAFSU. To ba lefi ga Muridansa su su koma ga wancan Muqaddamin da yafishi sani da daukaka, amma da sharadin kada su wulankata da lamarin na farko! Kuma karsu yanke ga barinsa. Masanin Allah Al ba'aqiliy ya fada a littafinsa "ira'ati shumusul Falakil Haqaakiqil Irfaniyyya": "Wanda ya Rika a hannun wanda ba Masani ba a Darika kamar ya zamo yana cikin masu izini ne wajen Talqini kawai, bai da izini wajen NIYABAH. Da yin tarbiyya da Raba Asrarai, Bari wanda ya Lakkana masa ya tsaida shi ne kan bafa wuridi kawai, misalin kamar dan aike ne da aka bashi wasikabai san ya karanta ta ba, koda ya Bude bazai fahimta ba. Muradin sa kawai ya isar da wannan Ijaza ne kawai ga waninsa, to ai Kaga abinda ya isar din nan yana nan a ingatacce, sai dai shi Dan Aiken bai san ya karanta ba ne haka wanda ya sadarwa, wato Muridin nasa- saboda shi ya jahilci abin ne kawai. Zaka ga ya karbi Wasikar yana juya ta yana girmama ta, ya kuma bada Lada akanta,
To anan shi wanda ya karba ya wajaba gareshi ya dau Wasikar nan ya tafi da ita ga wanda yake Masani da Isharorin wanda ya rubuto masa Wasikar don ya shiryar dashi har ya fahimci sashin abinda ke cikinta, anan sai ya amfana da ita, haka ya lazimce masa girmamashi da karramashi. Domin shine asalinsa kadai wajen Karrama yan uwa.
To yaje ya Jefar da kansa gaban har ya samu tahaqquqi da Allah don Allah acikinsa.
Manahilur Rashad tare da Shehu Atiku sanka
Comments
Post a Comment