ISIS TA YIWA BABBAN SUFI YANKAN RAGO A MASAR
Kungiyar nan mai daawar kafa Daular musulunci ta ISIS ta fitar da wani hoto dake nuna kashe wani tsoho dan shekara kusan 100 a duniya data ce an zartar da hukumcin sharia ne Kan Boka kuma Dujal.
Bayan fitar wannan hotuna ne aka gane cewa wannan tsoho ba wani bane face Babban Malami kuma mai gudun Duniya Sufi da kowa ke jin Maganarsa a Yankin Sainaa ta Masar wato Sheikh Sulaiman Abu Haraaz, wanda aka sace shia gaban gidansa kimanin wata daya data gabata.
Shidai wannan Sufi Jagora ne daya karar da rayuwarsa wajen waazi ga Kauyawan dake Sainaa na Masar, kuma an kasheshi tare da wani tsohon na Daban ta hanypar yi musu yankar Rago.
Dalilai na nuna cewa waazin Abu Haraaz da yake yawan yi kan watai da tunanin salafanci mai tsauri da Kafirta Musulmi da kuma hana Jamaa bin kungioyin Taaddabda Sunan Musulunci sune suka janyo akai masa wannan aika aika.
A wadancan Hotuna an nuna Shehin Sufin yana sanye da tufafi masu ruwan Lemo da a al'adar Kungiyar ta ISIS take sanyawa ga duk wanda zaa zartar masa da hukuncin kisa.
Comments
Post a Comment