Manahilur Rahad Tare da Shehu Atiqu Sanka




Amsar Tambaya ta 10
Kai sani cewa Sukarin nan na kwali da Shehu Tijani yai magana akansa kamar yadda yazo cikin littafin Ifadah Nazifi ya hakaitoshi a Yaqutatil faridah; cewa shehu Tijani RA an bashi labari ta hannun wasu matafiya cewa wannan Sukari ana yinsa ne da jinin da Kasusuwan Jaki da Alade, don haka sai shehu Tijani yace Haramun ne kamar Shan Giya, ya kuma dena shansa yabar Shan Ataya tun daga Ranar yai umarni ma aka Jefar da abinda ake dafashi cikin Rijiyar Zawiya.
To sai daga bisani wasu daga Sahabbansa makebanta da yake izina dasu sukai Tafiya sai suka Gano muhallin da ake yin wannan Sukari kuma suka tabbatar cewa babu wani abu da ake fada na Jini da kashi sai suka zo suka gayawa Shehu Tijani da hakikar abin, sai Yace dasu "ni dai na barshi saboda Allah kuma bazan koma ba, to anan Almajiran shehu Tijani suka rabu uku: wasu sun barshi gaba daya kamar yadda Shehun yayi, wasu kuma suka dawo suka cigaba da sha, wasu kuma ska zamo suna amfani dashi Jefi Jefi, kuma wannan duk a gaban Shehu Tijani ne bai taba Zargin wani ba. Izuwa wannan Nazifi yake ishara da fadinsa a Yakuta bayan fadin Bain:
(yayin da yakini yazowa s Tijani sai yace mu mun barshi don ubangijin halitta)
(daga sahabbansa akwai mai sha agabansa a zahiri, da mai barinsa kaf damai sha sama sama)
(bai zargi mai shansa ba Wala kuma wanda ya bar sha ba don dai budawa)
To bisa wannan Batijjane ya iya Sha ko ya barshi in yaso ba zargi akansa. WASSALAM.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY